Amurka Ta Bukaci Nijeriya Ta Canza Salo

0
774
Shugaba Muhammadu Buhari

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

DOMIN ganin an magance matsalar ‘yan boko haram, kasar Amurka ta shawarci Nijeriya ta canza salon yakin da take yi da ‘ya’yan kungiyar .

Wannan kiran na alamta cewa akwai gagarumar matsala a kokarin yaki da wadannan ‘yan boko haram .

Kamar dai yadda rahotanni suke bayyanawa musamman a wata tattaunawa da manema labarai ke yi a cikin shirin Talbijin na TVC mai suna Dandalin ‘Yan Jarida shugaban tashar ya tabbatar da cewa an kashe dubban sojoji a wannan yakin da ake na boko haram.

Ya kuma tabbatar da cewa akwai wani lokacin da ‘yan boko haram ke kokarin ba jama\’a bashi a Madagali ta Jihar Adamawa domin kawai a karshen lamari su samu goyon bayan jama\’a.

Hakazalika idan aka yi la\’akari da irin yadda ake kashe kudin gwamnati ta sunan yakin boko haram shi ma abin dubawa ne. Ga kuma kasar Amurka da ke da muhimmanci a cikin al\’amuran duniya baki daya.

Tambaya dai shi ne su wane ne ainihin jagororin wannan kungiya kuma ta yaya za a iya magance matsalar?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here