Ba Gaskiya Ba Ne Korar Malamai Dubu Hudu Da Dari Biyar

0
871
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa\'i na Jihar Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i, ta karyata cece-kucen da ake yi cewa wai ta kori Malaman makarantar da suka dauka kwanan baya har su dubu hudu da dari biyar duk zancen ba gaskiya ba ne.

Abin da hukumar kula da ilimin Firamare ta Jihar Kaduna ta bayyana shi ne ta tabbatar da daukar mutane dubu 11,395 daga cikin mutane 15,000 da aka tantancewa lokacin daukar aikin malantar

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kaduna Mista Samuel Aruwan ya fitar a Kaduna.

A nan gaba kadan za a sanar da daukar wadansu Malaman makaranta dubu 13,605 da hukumar Firamaren za ta yi nan gaba kadan, sanarwar ta ci gaba da cewa tuni hukumar ta karbi takardun neman aikin malanta har mutane dubu 19,000 kuma za a dauke su ba tare da tantama ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here