HANZARTA KAWO DAUKI NA GWAMNATIN TARAYYA: HUJJOJIN GANI DA IDO DA BINCIKEN JAMI’AN MA’AIKATAR MA’ADINAN RUWA TA KASA A YAYIN ZIYARARSU A JIHAR SAKKWATO
A kwanakin baya, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta hanyar aiken sakon gwamnatinsa mai suna ATM-SG (#SaveGoronyoDam) da ta shigo cik tsundum kan batun halin ni-‘ya-su da Dam din yake fuskanta, wanda shi ne yake bai wa jihar ta Sakkwato ruwa da ma makwabciyarta, jihar Kebbi.
Kungiyar goyon bayan Gwamnan ta dauki wannan dama inda take mika godiyarta ga gwamnatin tarayya kan sauraren kiran da Gwamnan ya yi a inda kwanan nan ta aiko da jami’an ma’aikatar ma’adinan ruwa ta kasa domin su binciko yadda lamarin yake.
Mun hakikance cewa, gwamnatin tarayya tare da goyon bayan jihar za su iya fito da tsare-tsaren ayyukan da za a gudanar wa Dam din na Gwaranyo don ganin an kawar da matsalar baki daya.