Mustapha Imrana Abdullahi
AN bayyana batun sabuwar dokar tsarin fansho da ake yadawa cewa wai Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya aikawa Majalisar dokokin Jihar da cewa duk Jita jita ce kawai da bata da tushe balantana makamai.
Ita dai wannan sabuwar dokar fansho jama\’a musamman ma\’aikata da kuma Iyalan su ba su murna ko kadan da ita, domin a cewarsu akwai dimbin matsaloli a tattare da ita musamman ga duk Wanda ya bar aikin Gwamnati a Kowane irin mataki.
Bayanan da suke fitowa daga Jihar Katsina a bangaren Majalisar na cewa majalisar dokokin Jihar Katsina ba ta karbi kudurin da ake ta cece ku ce a kan sa ba daga bangaren zartaswa ba.
Shugaban majalissar dokokin jihar Alhaji Abubakar Yahaya Kusada ne ya fadi haka inda yake cewa wannan jita jita ce ake yadawa wadda bata da tushe ballantana makama.
\” Ba wata magana makamanciyar wannan a majalissar , ya ce duk dokar da taje majalissar ba za’a zartar da ita ba har sai an saurari ra’ayoyin al’umma a game da kowace irin Doka ce\”.
Shugaban majalisa ya ci gaba da cewa idan da irin wannan doka tazo, majalisa dole sai an gayyato masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu, yan siyasa, ma’aikata da sauran jama’a domin su bayyana ra’ayinsu kafin a zartar da ita ta zama doka.
Shugaban majalissar dokokin ya Kuma yi kira ga al’ummar jihar Katsina da suyi fatali da duk wata jita jita mara tushe da ake yadawa.
Ya Kuma bayar da tabbacin cewa Majalisa da bangaren zartaswa ba za su yi duk wata doka wadda za tota sa al’umma cikin kuncin rayuwa ba ko abin da al’umma ba su bukata ba.