Direbobi Sun Yi Zanga Zanga-zangar Lumana A Babbar Hanyar Yola-Jalingo Saboda Karbar Na-goro

0
749
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Rahoton Rabo Haladu Da Saleh Shafi\’u
ZANGA-ZANGAR da direbobin motocin haya suka gudanar ta rufe babbar hanyar Yola-Jalingo, na tsawon awanni hudu, ba tare da direbobin sun bude hanyar ba, lamarin da ya tsaida harkokin zirga-zirga ababen hawa a babbar hanyar.
Daukar matakin zanga-zanga da rufe babbar hanyar da direbobin suka yi, ya biyo bayan zargin matsa musu da amsar na goro da ma tsarewar da jami\’an tsaro soji da \’yan sanda ke yi a kan babbar hanyar.
Daruruwan direbobin da suke zanga-zangar sunyi dandazo a garuruwan Taraba, Ganye, Jada a garin Mayo-Belwa, sun fara zanga-zanga agaban jami\’an tsaron \’yan sanda da suka kafa shingen bincike ba bisa qa\’ida ba, suna amsar na goro.
Wannan dai shine lamarin da ya kaiga direbobin suka zuciya sukace ba su yarda ba, abu kamar wasa ya zama mana tashin hankali sosai a gari, inji Usman Ahmadu wani mazaunin garin Mayo-Belwa.
Direbobin sun kuma zargi jami\’an tsaron soja da \’yan sandan da cewa a kowani lokaci sukan kafa shingaye a kan babbar hanyar, kuma su tilasta direbobin biyan naira 200 ko fiye kafin su wuce.
\”jami\’an \’yan sanda sun kafa shingayen binciken ababen hawa kamar yadda suka saba duk ranar kasuwar Mayo-Belwa, na basu naira 50, amma sukaqi su amsa, suna neman sai na basu naira 200, ni kuma naqi shine suka fara dukana.
\”Wannan direban da ya fusata shi ya fara rufe hanyar kamar yadda kake gani, babu inda za mu je sai an yi mana adalci kan wannan matsala\” inji daya daga direbobin.
Haka shima wani direban babbar mota da yace sunanshi Emmanuel Daniel ya ce \”jami\’an tsaro mafiyawan lokaci \’yan sandan SARS da sojoji da jami\’an VIO suna ajiye direbobin baya, jami\’an tsaro suyi yadda sukeso da kai.
\”a ranakun da kasuwanni ke ci jami\’an tsaron kan kafa shingayen bincike suna amsar na goro abin kunya soja ba zai amshi kasa da dari biyu a hanunka ba, haka kuma \’yan sanda da sauran masusa kayan Sarki\” inji Emmanuel.
Da yake magana kan wannan batu jami\’in hulda da jama\’a na rundunar \’yan sandan jihar Adamawa SP Othman Abubakar, ya ce tuni rundunar ta jinge jami\’ai domin kwantar da tarzoma a yankin.
Ya ce rundunar za ta gudanar da bincike game da zargin da direbobin ke yi wa jami\’an tsaro a hanyar, ya ce rundunar za ta hukunta duk jami\’in da ta samu da laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here