Akantoci Na Hada Kai Da Batagari A Yi Satar Kudi – Masari

0
569

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga daukacin kungiyoyi da cibiyoyin kwararru da su samar da dokokin da za su rika hukunta masu kunnen kashi da ke bata aikin da suke yi wa al\’umma.

Gwamna Masari ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaban cibiyar kwararrun akantoci ta kasa ( ICAN) Alhaji Sama\’ila Mohammad Zakari da ya kai wa Gwamnan ziyara a gidan gwamnatin Katsina.

Gwamnan ya yi bayanin cewa kwararru kamar Akantoci,masu sana\’ar zane-zanen Gini,Lauyoyi,’yan jarida,masu aikin gini,da masu aikin asibiti kamar Likitoci da unguwar zoma da sauran su da aniyar ganin an hukunta duk masu bata aikin.

Alhaji Masari ya fayyace masu cewa akwai bukatar wannan cibiyar akantoci ta tabbatar da hukunta ‘ya’yanta saboda irin yadda wasu mambobi ke hada kai da wadanda ba su da kishin kasa ana kwashe dukiyar jama\’a ba gaira ba dalili

Masari ya kuma ba su tabbacin cewa zai ci gaba da taimaka wa cibiyar musamman a bangaren horar da akantoci a Jihar Katsina.

Ya kuma yi masu alkawarin filin da za su gina matsugunnin cibiyar domin koyar da ilimin masu lissafin kudi da duk ayyukan da suka shafi hada-hadar kudi baki daya a babban birnin jihar .

Ya bayyana cewa a matsayinsa na Gwamnan Katsina ya dauki nauyin wasu akantoci su yi karatu a nan gida da kasar Dubai domin su samu kwarewa.

Tun da farko shugaban cibiyar akantocin na kasa Alhaji Sama\’ila Muhammad Zakari, cewa ya yi sun zo Katsina ne domin shaida wa Gwamnan irin ayyukan da suke yi a cibiyar.

Alhaji Zakari ya ce an kafa cibiyar ne a karkashin dokar kasa tun shekarar 1965. Ya yi godiya game da irin yadda Gwamna Masari ke taimakon shugaban cibiyar na jiha tare da mambobinsa baki daya.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here