Duniya Ta San Muhimmancin Nijeriya – Buhari

0
696
Shugaba Muhammadu Buhari

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a yanzu duniya baki daya ta san muhimmancin kasar musamman a Afrika da duniya.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai na kafar yada labaran muryar Amurka.

Inda ya ce kasancewar irin yadda duniya ta amince da Nijeriya shi ya sa shugaban Amurka Donald Trump ya dauki waya ya kira shi cewa ya tanaji kudi domin sun shirya sayar wa Nijeriya jiragen saman yaki don haka a tanaji kudi kawai.

\”Tun a lokacin mulkin Barrack Obama Nijeriya ba ta samu zarafin a sayar mata da jiragen yakin ba sai a yanzu, shugaban Amurka da kansa ya kira ni ya ce mu tanaji kudi don za a sayar mana da jiragen yaki da ba mu samu damar hakan ba a can baya\”.

Ya ci gaba da cewa sun yi kokarin a samo jiragen nan daga kasar Birazil da hadaddiyar Daular Larabawa amma suka ce wa Nijeriya ba za su iya sayarwa ko bayar da wannan jiragen ga wani ko wata kasa saboda a cikin yarjejeniyar da suka da Amurka kafin saye ta hana wannan, amma sai ga shi an kira ni cewa za a sayar mana da jiragen nan.

Buhari ya kuma ce ana nan ana kokarin tsattsara yadda za a yi wa ‘yan cin amanar kasa da suka kwashe kudin jama’a hukunci kamar yadda ya dace ta yadda kowane mi laifi za a tabbatar masa da laifinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here