Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Mutanen Da Rikici Ya Shafa

1
576
Shugaba Buhari a wata ziyrar aik a Filato

Saleh Shafi\’u, Daga Yola

GWAMNATIN tarayya ta tallafa wa jama\’ar da rikicin Fulani makiyaya da manoma ya shafa a yankin gundumar Dumne cikin karamar hukumar Song a jihar Adamawa da motoci uku na kayan masarufi.

Da yake mika tallafin kayan abinci da na gini ga mutanen yankin a garin Tende, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) wanda shugaban hukumar a jihohin Adamawa da Taraba Imam Abbani Garki, ya wakilta ya jajanta musu da aukuwar rikicin.

Garki ya ce tashin rikici a kowane lokaci ba zai warware matsala ba, ya ce zaman lafiya ya fi zama dan Sarki don haka ya bukaci jama\’ar yankin da su guji duk wani abu da zai kai ga tashin hankali domin samun ci gaba.

\”Tashin hankali ba zai taba magance matsala ba, kuma ba zai haifar muku da ci gaba a yankinku ba, saboda haka ku yi hakuri da juna domin samun zaman lafiya da ci gaba. Ba bukatarmu ba ne ko da wane lokaci sai mun taimaka muku da kayan abinci ko wani abin bukata ba, mu yi hakuri da juna rikici ba zai magance mana matsalolinmu ba\” inji Abbani.

Da yake bayani game da kayan tallafin da hukumar ta tallafa wa jama\’ar yankin da shi kuwa Abbani Garki, ya ce hukumar ta tallafa da manyan motoci uku da kayan abinci da suka hada da Masara, Gero, Shinkafa, kayan sawa, da kuma kayayyakin gini.

Ya ce kayan tallafin ba zai wadatar da jama\’ar da matsalar ta shafa ba, ya ce \”wannan  dai tallafi ne muka kawo muku domin mu rage muku wahalhalu da matsalolin da kuke ciki, amma ba domin mu mayar muku da abin da kuka rasa ba\”.

Imam Abbani Garki, ya shawarci \’yan siyasa da su cire harkar siyasa a duk lokacin da hukumar ke da bukatar tallafa wa wasu mutanen da rikici ya shafa, ya ce \”mu na kowa ne, ba mu daukar wani bangare a duk lokacin da za mu bada kayan tallafi\” inji Garki.

Da yake jawabi a madadin jama\’ar yankin tunda farko Mista Solomon Musa, ya ce wannan shi ne karon farko da suka samu kayan tallafi tun lokacin da rikici ya barke a yankin, ya yaba da cewa akwai jama\’a da dama da ba su kai ga gyara gidajensu ba.

Ya ce suna rokon da a ci gaba da ba su kayan tallafin musamman na gini ta yadda jama\’ar yankin za su samu damar gyara gidajensu da rikicin ya lalata.

Dama dai cikin watan Fabrairun da ya gabata ne aka samu tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin lamarin da ya kai ga mutuwar jama\’a da dama da kone garuruwan Fulani da na manoma kurmus.

 

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here