KUNGIYAR KWANKWASIYYA TA RARRABA KUDI NAIRA DUBU GOMA-GOMA DON JARI GA MATA 100 A JIHAR YOBE.

  0
  693
  Gwamna Ganduje Na Jihar Kano

  Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU

  KUNGIYAR  Kwankwasiyya a karkashin tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u

  Musa Kwankwaso wanda a yanzu shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tsakiyar Kano a majalisar dattijai ta kasa ta kai tallafin kudade dubu goma-goma ga mata 100 a Jihar Yobe don bunkasa sana\’o\’insu.

  Da yake jawabi a madadin madugun na kungiyar Kwankwasiyya Dokta Rabi’u

  Musa Kwankwaso, Alhaji Siraja Kwankwaso ya tabbatar da cewa wannan tallafi na daga cikin kokarin Dokta Kwankwaso wajen rage talauci a tsakankanin al\’umma mata da maza.

  Wakilin na Kwankwaso ya kara da cewar, sun ware mata 100 da za su amfana da wannan tallafi na kara jarin Naira dubu10 ga kowanne daga cikin matan da za su amfana don kara habaka sana\’o\’insu na tuyar kosai, karago ko kunu, dan wake, dinki da makamantansu.

  Ya ci gaba da cewar, sun zabi adadin matan da za su amfana da wannan tallafi ne a kusan kowacce daga kananan hukumomin jihar 17 inda suka kasa su ya zuwa shiyya uku na majalisar dattawa.

  Alhaji Siraja Kwankwaso ya kara da cewar, a yanzu haka wannan kungiya tasu ta Kwankwasiyya karkashin daukar nauyin jagoransu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

  sun bada irim wannan tallafi ga wasu matasa mata da maza fiye da dubu 8500, kuma nan gaba kadan suna da shirin kara bada wannan tallafi na karin jari ga mata kusan dubu 5 a Jihar Kano.

  Shi ma Malam Nuhu Sarina daya daga tawagar ta kwankwasiyya shawartar

  matan ya yi da su ririta dan cin da suka samu don amfanin kan su da na iyalensu.

  Daya daga cikin matan da suka amfana da wannan tallafi na dubu goma-goma a madadin dukanin matan Amina Sarkin Hausawa daga karamar hukumar Fika godiya ga kungiyar ta kwankwasiyya dangane da wannan tallafi da aka ba su, kana ta kuma ja kunnen \’yan uwanta mata da su kula da wannan jari da aka ba su don na gaba su amfana.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here