Wutar Lantarki : Wamakko Ya Ceto Kananan Hukumomi Hudu

0
734
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN kungiyar ‘yan majalisar Dattawan arewacin Nijeriya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya fara kokarin gyaran wutar lantarkin kananan hukumomin Gudu, Silame, Binji da Tangaza duk a Jihar sakkwato

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai magana da yawun Wamakkon da hulda da jama\’a Bashir Rabe Mani ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Takardar ta ci gaba da cewa wannan aikin samar da wutar lantarki ya zo a kan gaba saboda layukan wutar sun lalace ne shekaru biyu da suka wuce, wanda sakamakon hakan al\’ummomin na cikin duhun da ya jefa kananan hukumomin hudu cikin matsala.

Takardar ta ci gaba da bayanin cewa, Sanata Wamakkon ya tabbatar wa da daruruwan mutanen daga gundumomi 20 na yankin Gumbi da suka zo domin yi masa godiya bisa dalilin kokarin gyaran wutar da yake yi masu.

Sanata Wamakko da ke wakiltar mutanen yankin Sakkwato na Arewa ya kara jaddada cewa zai ci gaba da irin wannan kokari domin inganta rayuwar jama\’ar baki daya.

Wamakko wanda shi ne shugaban kwamitin kula da ilimin sakandare a Majalisar Dattawa ya bayyana gamsuwarsa da irin yadda jama\’a suke ba shi hadin kai da goyon baya tare da nuna kauna a kodayaushe.

Jama\’ar dai sun zo ne karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar Wamakko Alhaji Bello Buba Kauran Kimba da Hakimin Wajakke Alhaji Muhammadu Mailato Gumbo.

Dukkan su sun bayyana farin cikinsu tare da godiya ga irin wannan aikin da suka bayyana cewa zai daukaka darajar tattalin arzikinsu baki daya.

A wani labarin daban kuma Sanata Wamakko ya bayar da tallafin kudi Naira Miliyan biyar ga mutanen Nufawa,Tsamiyar Dila,Rumbu da wasu al\’ummomin a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa  da ke aikin gyaran hanyoyin ruwa ta hanyar aikin gayya

Sanata wamakko ya bayar da taimakon kudin ne lokacin da ya je ziyarar gani da idanu a wurin da ake aikin.

Ya bayyana cewa ya yi wannan ne domin su samu sukunin kammala aikin da zai amfani jama\’a, wanda hakan zai ba su damar yin maganin zaizayar kasa da kwararowar hamada baki daya.

Baki daya jama\’ar sun yi godiya kwarai ga dan Majalisar bisa wannan kokarin kawo masu daukin da za su samu saukin rayuwa.

 

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here