ZA MU CI GABA DA BUNKASA NOMAN ALKAMA A JIHAR KATSINA-HAJIYA RAHINATU MOHAMMED.

0
737

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

JAGORAR kungiyar mata manoman alkama ta Gozaki Kofar fada karamar hukumar Kafur, Hajiya Rahinatu Mohammed ta ce za su ci gaba da bunkasa noman alkama a wannan yanki tare da samar da kyawawan hanyoyi na sarrafa ta domin inganta tattalin arziki da dogaro da kai.

Ta yi wannan tsokaci ne a hirar su da wakilinmu a karshen wani taro na horar da sarrafa alkama wanda ma\’aikatar gona ta tarayya ta shirya wa mata manoman alkama a Kano, inda ta sanar da cewa Allah Ya albarkaci Jihar Katsina da mata manoma wadanda suke aiki rani da damina domin amsa kiran gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.

Hajiya Rahinatu ta ce manoman alkama mata da ke cikin wannan kungiya  suna aiki da murya daya sannan suna kara samun hanyoyi na dogaro da kai ta yadda zamantakewa za ta ci gaba da kasancewa cikin rufin asiri musamman a wannan lokaci da ake ciki na yanayin tattalin arziki.

Bugu da kari, ta yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, da ma\’aikatar gona ta jihar da kuma hukumar bunkasa aikin gona ta jihar wato KTARDA da su kara tallafa wa mata manoman alkama ta yadda za su ci gaba da bunkasa nomanta a fadin jihar kamar yadda suke yi a halin yanzu.

A karshe,Hajiya Rahinatu Mohammed  ta yi godiya ga ma\’aikatar gona ta tarayya bisa jagorancin  Daraktan Jihar Kano Alhaji  Muhammed Shehu Adamu saboda horon da suka bai wa mata manoman alkama wanda hakan ya taimaka wajen kara masu kwarin gwiwa wajen  kara nomanta da kuma sarrafata zuwa abubuwa daban-daban da ake yi da ita. Pix

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here