AL\’UMAR WAILARE SUN ROKI BADAMASI AYUBA YA GYARA MASU TANKIN SAMAR DA RUWA NA GARIN.

0
752
Gwamna Ganduje Na Jihar Kano

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AL\’UMAR garin Wailare da ke yankin karamar hukumar Makoda sun yi kira ga wakilin kananan hukumomin Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta tarayya da ya gyara masu tankin tattara ruwan da ya lalace ta yadda za su ci gaba da amfani da shi kamar yadda abin yake a baya.

Wannan roko ya fito ne daga Alhaji Uba Bello Wailare wanda aka fi sani da Alhaji Ubaliye, a wata ganawar su da wakilinmu, inda ya ce ko shakka babu idan dan majalisar ya gyara wannan tankin ruwa .na Wailare,za su kara samun wadataccen ruwa a wannan gari, sannan an saukaka wa al\’uma wajen samun ruwa domin amfanin yau da kullum.

Alhaji Uba Bello Wailare ya kuma nunar da cewa dan majalisa Badamasi Ayuba mutum ne wanda yake sauraron bukatun al\’umarsa, don haka yake kira gare shi a madadin daukacin al\’umar garin na Wailare domin ya taimaka wajen gyara wannan babban tankin ruwa domin amfanin al\’umar garin.

Haka kuma ya yi fatan cewa dan majalisar da sauran masu rike da madafun iko da ke wannan yanki za su dubi muhimmancin wannan gari na Wailare wajen gudanar da wasu karin aikace-aikace ta yadda al\’umar garin za su rabauta daga ribar dimokuradiyya kamar yadda ya kamata.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here