Hauwa Maina Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

0
1082

 

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

‘YAR wasan fim din Hausa mai suna Hauwa Maina ta rasu a daren ranar Laraba da ta gabata sakamakon ciwon bugun zuciya.

Kamar yadda rahotanni suka zo cewa ta rasu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Fitacciyar ‘yar wasan a rukunin masu wasan Hausa ta rasu tana da shekaru sama da 40 a duniy. Kamar yadda rahotanni suka bayyana an taba kaita asibitin kasa da ke Abuja inda aka yi mata jinya na takaitaccen lokaci.

Hauwa Maina ta fara fita a cikin fim din Hausa ne a wani fim da Saminu Muhammad Mahmud ya zama Daraktan sa a shekarar 1998.

Ta kuma samu nasarar fitowa a cikin fina-finai da dama da suka hada da fim din Sarauniya Amina, Gwaska da Maina wanda kamfaninta na \”Ma\’inta Enterprises Limited\” ya yi.

Hauwa Maina dai ta kasance daga cikin wadanda fuskokinsu suka yi suna a cikin shirin fim musamman a irin rawar da ta taka a cikin fina-finan Hausa na \”Sarauniya Amina da Bayajidda\”.

Ita dai Hauwa Maina ‘yar asalin Jihar Barno ce ta shiga harkokin fim ne bayan ta kwashe akalla shekaru ashirin a cikin harkokin wasannin nishadantar da jama\’a.

Ta kuma samu shiga da fitowa cikin fina-finai akalla 50, kuma ta samu kyaututtukan karramawa ta SIM a shekarar 2010, sai kuma kyautar \” Afro daga kasar Ingila a shekarar 2007.

Hauwa Maina ta bayyana wa kafar yada labarai ta ‘’Daily Trust’’ a wata tattaunawa da aka yi da ita inda ta bayyana yadda ta fara shiga harkar fim, bayan ta kammala karatun Difiloma a kan harkokin mulki a tsangayar ilimi ta kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna.

Ta kuma kasance tana hada aikin wuccin gadi a kafar labarai ta rediyon Freedom da kuma harkar hadawa da zama Daraktan fim.

\” sha a wace ta saka ni a harkar fim.a matsayina na daliba, kuma da dangantakar abokantakar iyali, Salisu Salinga, na zuwa ziyara sannan sai ya ce zai je inda ake shirin fim sai ya ce mu tafi tare.\” Ina tambaya me lokashin ke nufi, sai ya ce mini wuri ne inda ake shirya fim don ban sani ba shi ma yana shirya fim.

\”Sai mamaki ya kama ni har nake ce masa ina son in zama mai shirin fim, kodayake ba na tsmmanin zan iya, sai ya ce za ki iya mana. Amma sai baki.A wani lokacin ma ina ta tunanin yadda hotona zai kasance a cikin fim da kuma a kan tituna kuma ina tunanin shin sako nawa zan aika wa jama\’a ta wannan hanyar.

\”Sai muka yi dariya ya tafi. Dan lokaci kuma sai ya dawo a cikin sauri ya tambaye ni ko da gaske nake yi idan da gaske ne zai gwada ni\”.inji hauwa Maina.

Allah ya gafarta mata kurakuranta, ya sanya ta cikin rahamarSa, amin.

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here