Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SAKAMAKON wata takaddamar da ke kara ruruwa tsakanin mahukunta da masu sana\’ar busasshen itacen Girki a Kaduna yanzu lamarin ya haifar wa dimbin jama\’a shiga cikin wani mawuyacin hali musamman a cikin garin Kaduna da kewaye.
Su dai masu sana\’ar itacen suna kokarin tsare jama\’arsu da ke shigowa da itacen girki saboda kamar yadda lamarin yake tamkar suna yajin aiki ne sakamakon korafin da suke yi na matsatsin dokar da aka sa har ma da batun haraji.
Kamar yadda wakilinmu ya bincika lamarin ya samo asali ne sakamakon irin dokar hana shiga da itace da kuma gawayi cikin garin Kaduna .
Kamar yadda wakilinmu ya zagaya a wasu wurare musamman hanyoyin shiga garin Kaduna ya ga irin yadda masu sana\’ar suke ajiye itacen da suka dauko daga dajin da suke dauko itacen suna shiga cikin garin Kaduna domin sayarwa.
Sai su ajiye itacen a can bayan gari inda za ka ga dalar itace a dukkan hanyoyin shiga garin Kaduna da suke sauke itacen da suka dauko daga daji.
Hakika wannan mataki da gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka da kuma su masu sana\’ar sayar da itacen suka dauka na yin yajin aikin shigowa da sayar da itacen tsawon wata daya matakin ya jefa jama\’a cikin wahala da kaka-ni-ka-yi saboda karancin abin wuta ga masu yin girki.
Ita dai gwamnati tana kokarin tsare daji ne daga masu sare saren itace su kuma masu sana\’ar dauko itace daga daji suna sayarwa a cikin gari suna ganin taimakawa suke.
Sai dai akwai wata matsala ta kwaratowar hamada wanda babban abin da ke haifar da hakan shi ne matsalar rashin itatuwa a cikin gari da kuma daji.
Wata sabuwa kuma masu sana\’ar sayar da kananzir da iskar gas da ake girki da ita suna ganin kakarsu ta yanke saka suna sayarwa da jama\’a kan farashin da suka ga dama.
A waje daya kuma wakilinmu ya zagaya cikin gari domin jin ta bakin jama\’a kusan duk wadanda aka tattauna da su suna korafin cewa talaka ne ya shiga wahalar rashin itacen girki musamman ganin yana samun abin da zai ci ne ta hanyar amfani da itacen girki da yake saye daga masu kawo shi.
Fata dai a samu yin masalaha a tsakanin bangarorin biyu domin talaka ya samu sauki.