Masari Ya Amince Da Yin Sababbin Tituna A Musawa, Dan Ali-Marabar Dan Ali

0
638

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

 

GWAMNATIN Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince da a sa wa Titunan Musawa, Dangani, Dan Ali zuwa Marabar Dan Ali kwalta.

Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri Injiniya Tasi\’u Dandagoro ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa karo na uku wanda aka yi karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari.

Injiniya Tasi\’u Dandagoro ya ce za a sanya wa titin dukkan abin da ya dace domin ya yi daidai da tsarin ka\’idar gina titi.

Kwamishinan na ayyuka da gidaje ya kuma yi bayanin cewa za a gina Dam a garin Danja da ke karamar hukumar Danja a kan kudi Naira Biliyan Bakwai domin yin amfani da shi wajen ayyukan yau da kullum da kuma noman rani.

Injiniya Doguru, ya ce za a samar da wadansu Dam dam guda 10 za kuma a gyara wadansu Dam-dam guda 10 a kananan hukumomi 20 a fadin jihar.

A nasa bangaren mai ba Gwamna shawara a kan harkar samar da wutar lantarki ya bayyana cewa Asibitin Janar Amadi Rimi tuni aka amince da mayar da shi Asibitin koyarwa domin daliban jami\’ar Jihar ta Umaru Musa Yar\’Aduwa da ke karatun Likita su yi amfani da shi a matsayin Asibitin koyarwa.

Sauran ayyukan da aka tattauna a kansu a lokacin taron majalisar zartarwar sun hada da kafa gidauniyar lafiya ta Katsina, batun kafa babbar makarantar ayyukan unguwar zoma. Sai batun kafa cibiyar masu yoyon fitsari da dakin gwaje-gwajen kiwon lafiya da dai sauran su.

Kwamishinan yada labarai, al\’adu da harkokin cikin gida Alhaji Hamza Muhammad Borodo wanda shi ne ya jagoranci taron manema labaran ya sanar da kafa kakkarfan kwamitin yaki da miyagun kwayoyi.

Hamza Borodo ya ce gwamnatin APC ta damu kwarai bisa halin da matasa suke ciki wanda har da mata a kan ta\’ammali da miyagun kwayoyi inda ya tabbatar da cewa gwamnati a shirye take domin samar da dukkan abin da ake bukata domin kwamitin ya gudanar da ayyukansa ta yadda za a samu magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here