Masu Raba Wa Kafar Sadarwa Da Sunan ‘Yan Jarida Ba Mambobinmu Ba Ne – NUJ

0
597

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

HADADDIYAR  kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa masu rabawa a dandalin sadarwa suna cewa su tsofaffin ‘yan jarida ne ba mambobin kungiyar ba ne.

Wannan na kunshe ne a cikin takardar bayan taron da kungiyar ta gudanar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da irin yadda masu rabawa da sunan ‘yan jarida suke gudanar da ayyukan su a kafar sada zumunta wanda abin da suke yi bai yi kama balantana yin daidai da aikin jarida ba.

Takardar ta kuma tattauna a lokacin taronta na wata-wata kan batun yadda ake kashe mutane a Jihar Banuwai inda har aka kashe mutane a coci sun kuma shawarci mahukunta su hanzarta yin abin da ya dace domin kawo karshen lamarin.

A cikin takardar bayanin bayan taron ‘yan jaridar sun kuma yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Malam Nasiru El -Rufa\’i, kan ayyukan raya kasa domin jin dadin jama\’a inda suka ce an samu sahihan ci gaba a bangaren Ilimi da gina hanyoyi

Kungiyar ta kuma jajanta wa tsohon shugaban kungiyar na jiha Mista Andrew Fadason game da mutuwar mahaifinsa Mista Aboki Fadason.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here