Muna Neman Jama\’a Su Tallafa Da Jini Ga Mutanen Da Harin Bom Ya Shafa -Bindow

0
771
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Saleh Shafi\’u, Daga Yola

GWAMNA Jihar Adamawa Sanata Umaru Bindow Jibrilla, ya bukaci jama\’ar jihar da su taimaka da jini kyauta ga jama\’ar da tashin bama-bamai ya rutsa da su a garin Mubi, gari na biyu mafi girma a jihar.

Wannan nemn taimakon jinni na kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da babban mai taimaka wa gwamnan kan kafofin sadarwa Macauley Hunohashi, ya aike wa manema labarai, ta ce tuni gwamnatin ya ziyarci mutanen da suka jikkata da ke amsar magani a babban asibitin FMC.

Sanarwar ta ci gaba da cewa \”wannan yanayin da jama\’a suke ciki, ina rokon jama\’a da su taimaka su bada jini kyauta ga mutanen da abun ya shafa, da suke amsar magani a babban asibitin FMC Yola\” inji sanarwar.

Ta ce Gwamnan ya dakatar da zaman majalisar zartaswar da dama bisa al\’ada aka saba gudanarwa duk ranar Laraba, ta ce maimakon haka Gwamnan ya jagoranci mambobin majalisar wajan jajanta wa iyalan mutanen da harin ya shafa. \”Wannan abun bakin ciki da Allah-wadai ne, kuma aikin matsorata ne da ba za mu amince da shi ba\” inji Bindow.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da kayan magunguna a babban asibitin Mubi, inda ake ci gaba da kula da mutane sama da hamsin da suka jikkata sakamakon tashin bama-baman.

Sanarwar ta kuma yaba wa babban asibitin FMC Yola, da kungiyoyin sa-kai da suke gudanar da aikin ceto rayuwar mutanen, ta ce kokarinsu abin a yaba ne.

Da yake maida jawabi shugaban babbar asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola (FMC) Farfesa Muhammad Auwal, ya ce kwararrun likitoci da kungiyoyin sa-kai da ma mambobin kungiyar bada agajin Read Cross, sunanan domin bada kulawa ga marasa lafiyar.

\”Ina mai tabbatar maka ba mu da matsala, kuma komai na tafiya bisa tsarin kulawar kwararrun likitocinmu\” inji Farfesa Auwal.

Wannan na zuwa ne lokacin da gwamnatin tarayya ta umurci jami\’an tsaron da su tsaurara matakan tsaro a kasuwanni da sauran wuraren ibada a garin Mubi, domin hana sake aukuwar lamarin.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bada umurnin haka cikin wata sanarwar manema labarai da maitaimaka mishi kan kafofin sardarwa Laolu Akande, ya sa wa hannu, ta kuma umarci hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta gaggauta samar da magunguna da sauran kayayyakin agaji ga mutanen da harin ya rutsa da su.

Kawo yanzu dai mutane 48 suka mutu sakamakon tashin bama-baman biyu, wasu mutanen sama da hamsin kuma sun jikkata, wasu biyu na cikin matsanancin hali a asibitin FMC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here