Isah Ahmed, Jos
ALHAJI Danladi Garba Pasali shi ne shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organization. A wannan tattaunawa da ya yi wakilinmu kan maganar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi cewa matasan Nijeriya cima zaune ne, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ta murda wannan magana. Har ila yau ya yi tsokaci kan amincewar da shugaba Buhari ya yi, na tsayawa takara a zaben shekara ta 2019 da yadda wasu manya a Nijeriya suka fito suna cewa ba za su goyi bayan shugaba Buhari ba, a zaben na shekara ta 2019. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
GTK; A ‘yan kwanakin nan mutane da dama suna ta koke-koke kan bayanin da shugaba Buhari ya yi na cewa matasan Nijeriya cima zaune ne, mene ne za ka ce kan wannan al’amari?
Danladi Pasali; Wato duk wanda ya saurari abin da shugaba Buhari ya ce kan wannan al’amari zai fahimci cewa ‘yan adawa ne suka murda bayanin da shugaba Buhari ya yi. Domin bayanin da suke cewa ya yi ba haka ya fada ba.
Shugaba Buhari yana bayani ne kan wadansu matasan Nijeriya kuma abin da ya fada, ba karya ba ne gaskiya ce ya fada.
Ba irin wadannan matasa da shugaba Buhari yake nufi ne ba, aka yi amfani da su a boko haram? Ba irin su ne suke garkuwa da mutane ba?
Babbar damuwar da ta sanya suka shiga cikin irin wadannan abubuwa akwai wasu miyagu da suka sace kudaden Nijeriya suka kai kasashen waje suka boye, maimakon su bude manyan kamfanoni a Nijeriya ko kuma su karfafa wa matasa gwiwa su koma gona.
Wannan shi ne abin da shugaba Buhari ya fito da shi ya sanya matasa suka koma gona. Don haka wannan magana, magana ce ta PDP domin idan ka duba wannan magana, wani jigo a jam’iyyar PDP ya fito ya bayyana cewa wannan magana ta matasa da Buhari ya yi da PDP ta fito tana ta maganganu a kai, ba haka ya fada ba.
Kuma duk masu cewa hankalin matasan kasar nan ya tashi kan wannan magana da shugaba Buhari ya yi ‘yan adawa ne, kuma ba gaskiya suke fada ba, domin matasan kasar nan suna nan tare da Buhari.
Ko a makon nan a Jigawa matasa sama da dubu 700 ne suka fito suka ce suna murna da amincewar da shugaba Buhari ya yi, na cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2019.
Sai dai a ce wasu kalilan mutane ‘yan barandar barayin kasar nan. Wadanda idan barayin sun debo kudaden kasar nan suke ba su wani abu, sune suke ta yada karairayi kan wannan magana.
GTK; A matsayinka na shugaban mkungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organization mene ne za ka ce dangane furucin da Shugaba Buhari ya yi na cewa zai sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na shekara ta 2019?
Danladi Pasali; Wato na farko za mu ce mun gode Allah, dama fafutukar da muke ta yi kenan. Muna ta kira kan shugaba Buhari ya amince ya sake tsayawa zaben shekara ta 2019, domin ba zai yiwu a ce irin dimbin ayyukan da ya faro na raya kasa, a ce ba zai sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019 ba.
Don haka a wannan kungiya a muka rika yawo a duk fadin kasar nan, muna shirya zanga-zanga a wurare daban-daban, tare da yin kira a gidajen rediyo da jaridu kan shugaba Buhari ya amince ya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019 mai zuwa.
Don haka mu muna ganin wannan amincewa da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi, na sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019 kamar addu’armu ce Allah ya amsa.
GTK; A kwanakin baya wasu tsofaffin janar-janar na soja a Nijeriya, sun fito sun nuna cewa ba za su goyi bayan shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019 ba. Mene ne za ka kan wannan mataki da wadannan tsofaffin janar-janar suka dauka?
Danladi Pasali; Abin da nake son ka gane shi ne dukkan wadannan tsofaffin janar-janar da wasu tsofaffin shugabanni da wasu marasa kishin kasa. Dama ai ba su ne suka bai wa shugaba Buhari zabe ba, talakawan Nijeriya ne suka fito suka zabe shi shugabancin kasar nan, domin su ne suke sonsa. Kuma dukkan wadannan tsofaffin shugabanni da suke adawa da shugaba Buhari kashi 80 bisa 100 ‘yan jam’iyyar PDP ne. Don haka ba wani abin mamaki ba ne, don sun fito sun ce ba za su amince shugaban kasa Buhari ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan ba.
Kuma ina son ka gane cewa binciken da wannan gwamnati take yi, kan cin hanci da rashawa da kuma yadda wadansunsu ba sa biyan harajin kamfanoninsu duka wadannan abubuwa suna damunsu.
Bayan haka kuma a saninmu ne cewa rijiyoyin man wadansu daga cikinsu lokacinsu ya riga ya kare. Maganar sabunta wadannan rijiyoyin mai wani aiki ne mai wahalar gaske a wajensu a zamanin wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari.
Kuma idan ka dubi wadannan tsofaffin janar-janar rikice-rikicen kabilanci da addini da ake fama da shi a garuruwansu ana zargin suna da hannu a ciki. Don haka ba abin mamaki ba ne don sun fito sun ce ba za su amince shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2019 ba.
Idan ka lura duk mutumin da ya ce baya kaunar shugaba Buhari, idan ka dube shi za ka ga ko tsohon barawo ne ko tsohon macuci ne irin wadannan mutane ne ba sa son Buhari.
Don haka mu talakawan Nijeriya da muke neman shugaba Buhari ya kafa mana ginshiki a Nijeriya, muke kaunarsa kuma za mu ci gaba da kaunarsa. Don haka a zaben shekara ta 2019 ina tabbatar maka cewa babu wani kokonto cewa shugaban kasa, zai sake lashe zaben kujerar shugabancin kasar nan.
GTK; Idan muka dawo nan jihar Filato mene ne za ka ce kan sake fitowa takara ta zaben Gwamnan jihar Filato a zaben shekara ta 2019 da Gwamna Simon Bako Lalong ya yi?
Danladi Pasali; Wato Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ina son na tabbatar maka cewa a tarihin jihar Filato, bayan tsohon Gwamnan jihar Solomon Lar ba a taba samun Gwamnan da ya hada kan jama’ar jihar Filato ba, kamar Gwamna Simon Lalong. Sakamakon kokarin da Gwamna Lalong ya yi yau jama’a ko ina a Nijeriya da kasashen waje suna son su zo jihar Filato, don gudanar da harkokinsu. Don haka idan Gwamna Lalong ya ce bai tsaya takarar Gwamnan jihar Filato a zaben shekara ta 2019 ba, kamar ya ci amanar al’ummar jihar Filato ne. Don haka muna tare da shi kuma ina son in tabbatar maka a zaben Gwamna na shekara ta 2019, babu gurbi a kujerar Gwamnan jihar Filato, domin mu ba mu san kowa ba, sai Gwamna Lalong.
Domin yau a jihar Filato kowa yana shiga duk inda ya ga dama a jihar. A zamanin gwamnati PDP da ta gabata a jihar Filato, abin ba haka yake ba. A lokacin a jihar Filato Bahaushe musulmi yana tsoron ya shiga unguwar kiristoci. Kiristoci suna tsoron su shiga unguwar musulmi, amma yanzu duk wannan tsoro ya kau. Don haka ko’ina a jihar Filato, musulmi da kirista sun zama daya ana zaune lafiya sun zama ‘yan uwa kamar yadda ake a da. Don haka wannan abu na kawo zaman lafiya da Gwamna Lalong ya yi a jihar Filato, ya nuna cewa shi ne shugaba na kwarai.
GTK; Karshe wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Nijeriya?
Danladi Pasali; Sako na ga jama’ar Nijeriya shi ne shugaban kasa Buhari ya bude mana hanyoyi na ci gaba da dama a Nijeriya, musamman shirin bayar da rancen noma na babban bankin Nijeriya.
A yanzu maganar da nake gaya maka a karkashin wannan kungiya kadai a shirin harkokin noma da muke yi. Mun dauki matasa miliyan daya da muka hada hannu da ma’aikatar gona ta tarayya da babban bankin Nijeriya don bai wa wadannan matasa rancen noma a daminar bana.
Wani babban abin alheri da wannan gwamnati ta yi, yanzu idan ka tafi kasashen waje har Afrika ta kudu za ka ga shinkafar da aka noma a Nijeriya ana sayarwa. Ka ga wannan wani babban abin alfahari ne ga Nijeriya.
Bayan haka a tafiyar da shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a ‘yan kwanakin nan, ya je ya kulla wata yarjejeniya da kamfanin mai na Shell, a inda za su zo Nijeriya su sanya hannun jari na kudi Dala Biliyan 15 don kafa matatar mai a Nijeriya. Wannan ya nuna cewa har yanzu kasashen duniya suna girmama shugaba Buhari suna ganin darajarsa.
Kuma yanzu kudaden ajiyarmu na asusun waje sun kai sama da Dala Biliyan 48, wannan ne ya jawo kasashen duniya suke rige-rigen zuwa don zuba jarinsu a Nijeriya.