Mustapha Imrana Abdullahi Daga
RAHOTANNI daga karamar hukumar Numan ta Jihar Adamawa sun bayyana cewa akalla mutane talatin ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da \’yan bindiga suka kai wa kauyuka biyar.
Rahotannin sun ce an ga wadansu mutane da ake zargin cewa Fulani ne da bindigu, adduna inda kamar yadda rahotannin suka bayyana an kai hari ga kauyuka biyar wanda sakamakon hakan rayukan mutane a yanzu talatin ne aka tabbatar sun salwanta.
Kuma ana nan tuni an bazama domin neman jama\’a da suka shiga daji domin tsira da rayuwarsu.
Kamar dai yadda bayanai daga karamar hukumar Numan suka bayyana cewa an kone wasu kauyuka biyu sannan mutane da yawa sun tsere daga gidaje su inda suka shiga daji domin tsira da rayukansu.
Sai dai kungiyar Miyatti Allah ta fito fili ta bayyana cewa abin da ake fadi na cewa wai Fulani ne ba gaskiya ba ne domin kowa ya san Fulani suna saba sanda ne ba bindiga ba.
\”Don haka ya dace a rika gudanar da bincike kafin a dora wa Fulani laifin abin da ba su yi ba\”.inji Miyatti Allah.