Mustapha Imrana Abdullahi
MAJALISAR masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa ta bayyana tube rawanin Alhaji Mustapha Sule Lamido a matsayin Hakimin Bamaina a karamar hukumar Birnin kudu.
Malam Ahmadu ya bayyana hakan a madadin masarautar inda ya ce bayan dakatarwar da aka yi wa tubabben Hakimin, bincike ya tabbatar da cewa Mustapha Sule Lamido ya jefa kansa a cikin harkokin siyasa.
Masarautar ta Dutse ta ce nan ba da dadewa ba za a aike da sabon Hakimin da zai jagoranci al\’ummar Bamaina da ke karamar hukumar Birnin kudu.
Kamar dai yadda aka sani hukumar EFCC na tuhumar Alhaji Sule Lamido tare da dansa Mustapha Sule Lamido da kuma wani Hakimin da almundahanar kudi.