AN GUDANAR DA ZABEN SHUGABANNIN APC NA MAZABU NA KARAMAR HUKUMAR LERE LAFIYA

  0
  760
  Masu layin zaben shugabannin APC a Lere

   Isah Ahmed, Jos

  A yayin da aka gudanar da zaben shugabannin  jam’iyyar APC na mazabu a dukkan jihohin Nijeriya a ranar asabar din nan. Jam’iyyar  APC reshen karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna  ta gudanar da nata zaben shugabannin  a dukkan mazabu 11, da ake da su a karamar hukumar.

  Kusan dukkan shugabannin jam’iyyar an sake zabensu, don cigaba da rike kujerunsu, bayan da shugabanni da masu ruwa da tsaki  na jam’iyyar suka amince da yin hakan.

  Da yake zantawa da wakilinmu kan yadda aka gudanar da wannan zabe, wani kusa a jam’iyyar Alhaji Mas’udu Ahmed Yusuf Saminaka da ya fito daga mazabar Abadawa da ke wannan karamar hukuma,  ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da wannan zabe.

  Ya ce yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya ya nuna cewa Jam’iyyar APC daya ce, a karamar hukumar.

  Ya yi  kira ga magoya bayan jam’iyyar  su kara jajarcewa wajen bai wa wannan jam’iyya goyan bayan, musamman ganin irin ayyukan raya kasa, da Gwamna Nasiru El-Rufa’i yake yi a karamar hukumar.

  Shi ma a zantawarsa da wakilinmu shugaban jam’iyyar ta APC na mazabar Abadawa  Abdurra’uf  Umar Federe da aka sake zaba ya bayyana godiyarsa ga dukkan ‘yan  jam’iyyar na mazabar Abadawa kan damar da suka kara ba shi na shugabancin jam’iyyar.

  A zantawarsa da wakilinmu daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a mazabar Dan Alhaji,  Shehu Mato ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda suka gudanar da wannan zabe lafiya a mazabarsa ta Dan Alhaji.

  Ya ce mun gudanar da wannan zabe kamar yadda doka ta ce,  inda jama’a suka yi layi suka zabi abin da suke so.

  To amma a zantawarsa da wakilinmu wani kusa a jam’iyyar ta APC a karamar hukumar Lere, kuma mai taimaka wa dan majalisar wakilai ta tarayya na mazabar karamar hukumar Lere,  Sani Zubairu Garko ya bayyana cewa wannan zabe da aka gudanar akwai tubka da warwara a ciki.

  Ya ce domin tun da farko  sun san cewa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya  zauna da ‘yan majalisar wakilai na tarayya na jihar Kaduna da ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun daidaita kan cewa dukkan shugabannin jam’iyyar APC na mazabun jihar, kowa ya zauna kan kujerarsa.

  Ya ce don haka maganar zaben shugabannin mazabu na APC da ake cewa an yi a karamar hukumar Lere, akwai wata manufa a cikin mutanen da suke cewa sun gudanar da wannan zabe.

  ‘’Idan aka ce za a sanya son zuciya a cikin wannan jam’iyya za a haifar mata da da marar ido. Don haka muna takaici kan wannan al’amari da ya faru. Muna kira ga iyayen wannan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki na  jam’iyyar  su lura da masu shirin rusa wannan jam’iyya, su dauki mataki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here