Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ya bayyana wa taron \’ya\’yan jam\’iyyar APC cewa Sanatoci uku da suka fito daga jihar Kaduna ne suka dakile batun cin bashin bankin duniya na Dala 350 da Jihar ta kammala shirin samowa domin yi wa jama\’ar Kaduna ayyukan raya kasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron karbar wadansu jiga jigan PDP da suka koma APC da kuma ba \’yan takarar shugabannin kananan hukumomi 23 tutar jam\’iyya da shugaban APC na kasa John Oyegun ya ba su a filin wasa na Ranchas da ke Kaduna.
Gwamna El- Rufa\’i ya ce duk aikin da ya kamata a yi sun rigaya sun kammala sannan majalisu biyu na tarayya su sha shida har da \’yan PDP a cikin su duk sun amince a ciyo bashin kuma \’yan Majalisar dokokin Kaduna ma tuntuni sun amince da bashin.
\”Amma sai ga shi makiyan al\’ummar Jihar Kaduna su uku Suleiman Hunkuyi, Shehu Sani da La\’ah saboda kiyayyar mutanen Kaduna suka dakile batun a majalisa, don haka ya dace jama\’ar Kaduna baki daya su tabbatar masu da matsayinsu a lokacin zabe\”.
\”In sun shigo ku aske gemun daya, dayan kuma ku yi masa aski\”.
Ya kuma bayyana wa jama\’a irin dimbin ayyukan da suka yi wa jihar inda ya ce sun bayar da kwangiloli guda 1293 a jihar.
Ya ce a yankin tsakiyar Kaduna an bada kwangila 555 a kudancin Kaduna Kuma 338 sai yankin shiyya ta daya 392, duk dimbin kwangiloli ne da aka yi wa kasa aiki domin rayuwarsu ta inganta
Ya kara da cewa sun so ne duk inda ba a kammala aikin da aka bayar ba a kammala su cikin wannan bashin da muka nema daga bankin duniya amma sai Sanatocin Kaduna uku suka dakile batun a majalisa duk da \’yan Majalisar wakilai sha shida sun amince muna cewa Allah ya yi masu albarka, su kuwa da suka hana a ciyo bashin Allah ya tsine masu.
A wurin gagarumin taron an karbi yayan PDP da suka canza sheka zuwa APC da suka hadar da tsohon shugaban ma\’aikatan gidan gwamnati Yahaya Aminu daga Zariya sai Hajiya Saudatu Sani tsohuwar \’yar majalisar wakilai daga Lere
An kuma mikawa daukacin \’yan takarar shugabannin kananan hukumomi 23 na Kaduna da suka tsaya a karkashin APC tutar jam\’iyya.