APC Ta Gudanar Da Zaben Unguwanni A Adamawa

    0
    745
    I G Na \'Yan Sandan Najeriya
     Saleh Shafi\’u, Daga Yola
    JAM\’IYYAR APC mai mulki ta gudanar da zaben sabbin shugabannin jam\’iyyar a matakin unguwanni a jihar Adamawa, wanda ya gudana lami-lafiya in ban da matsalolin rashin isowar malaman zabe kan lokaci a wasu unguwannin.
    Rahotannin da ke fitowa daga sassan kananan hukumomin jihar 21, na nuni da cewa zaben ya gudana lafiya a wurare da dama, koda dai wasu mambobin jam\’iyyar sun koka da cewa ba su samu damar kada kuri\’ar ba.
    Shi ma dai kakakin majalisar dokokin jihar Honarabul Kabiru Mijinyawa, ya ce abin farin ciki ne yadda zaben ya gudana lami-lafiya a jihar.
    Ya ce \”na yi farin cikin ganin yadda zaben shugabannin jam\’iyyar matakin unguwanni ya gudana lafiya ba tare da samun wata matsala ba, wannan abin farin ciki ne, da ke nuni da hadin kan \’ya\’yan jam\’iyyar APC a jihar\” inji Kakakin majalisar.
    Da yake magana game da koke-koken da wasu ya\’yan jam\’iyyar ke yi kuwa Kakakin majalisar ya ce \” dama zabe ba a raba shi da haka, haka shi ne dimokradiyya, kuma ka san kowa na da \’yancin fadin albin da yake so\”.
    Masu kada kuri\’a a mazabar Wuro-Hausa, dake karamar hukumar Yola ta arewa sun koka da cewa ba a yi zabe a mazabar ba, suka ce sun dauki lokaci mai tsawo suna jira ba tare da malaman zaben sun iso ba.
    \”ka ganmu mun dauki lokaci mai tsawo muna jira, amma har yanzu malaman zaben ba su iso nan mazabar ba\” inji jama\’ar.
    Da yake magana game da yadda aikin zaben ke gudana kuwa shugaban kwamitin gudanar da zaben Musa Mahmoud, ya ce wurare da dama da suka ziyarta zaben ya gudana yadda ya dace, ba kamar yadda aka zata da farko ba.
    \”ba mu tsammaci zaben zai gudana haka ba, yadda ya yi zafi bamu dauka a yi a gama lami-lafiya haka ba, muna yiwa Allah godiya\” inji Mahmoud.
    Da yake magana game da koke-koken rashin isowar makaman zabe a kan lokaci kuwa shugaban kwamitin zaben ya ce \”babu mazabar da ba za\’ayi zabennan, duk inda aka samu jinkiri zamu tabbatar an magance matsalar\” injishi.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here