Bangaren Kwankwaso Ya Yi Zabensa Daban

  0
  692
  Gwamna Ganduje Na Jihar Kano
  Mustapha Imrana Abdullahi

  RAHOTANNI daga jihar Kano da ke arewa maso Yamma na cewa bangaren Kwankwaso Ya gudanar da nasa zaben fitar da shugabannin jam\’iyyar APC reshen Jihar.
  Koda yake bangaren Gwamnan mai ci Abdullahi Umar Ganduje bisa jagorancin Bashir Karaye sun gudanar da nasu zaben.
  Shi dai bangaren Kwankwaso bisa jagorancin Umar Doguwa sun tabbatar da nasarar yin zaben shugabannin a dukkan kananan hukumomi 44 da ke da yawan mazabu 440 a fadin Jihar.
  Umar Doguwa ya ce za su aike ne da sunayen shugabannin da suka zaba zuwa ofishin jam\’iyyar na kasa saboda jami\’an jam\’iyyar da aka turo domin gudanar da zaben da kuma jami\’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) duk sun shaida yin zaben nasu.
  Doguwa ya Kuma ce an yi zabe cikin kwanciyar Hankali da lumana ba tare da hatsaniya ba. Kuma an samu nasara ne sakamakon kokarin da aka yi na barin jama\’a su tabbatar da yancinsu kamar yadda doka ta ba su

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here