Masari Ya Halarci Sallar Jana\’izar Liman Muhammad Lawal  

0
522
 Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari na cikin dubban jama\’a da suka halarci Jana\’izar Marigayi Limamin babban amasallacin cikin garin Katsina Liman Muhammad Lawal.
Liman Gambo Ratibi ne ya sallaci gawar inda aka yi kabbarori hudu kamar yadda ya zo a Sunnah, sannan aka sallame.
Gwamna Masari yaje ne tare da mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu da sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa da kuma sauran Yan Majalisar zartaswa na Jihar.
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, da wasu Hakimai da masu rike da sarautun gargajiya na daga cikin wadanda suka halarci sallar Jana\’izar.
Filin kangiwa a nan ne aka yi sallar Gawar ya Kuma cika ya batse da Dan Adam da suka halarci sallar
Gwamna Masari yaje fadar Sarkin Katsina inda ya jajanta Masa a kan rashin Limamin da aka yi.
Gwamna Masari ya bayyana marigayin da cewa mutum ne mai hakuri, yakana tare da tsatseni, saukin kai tare da tsoron Allah.
Masari ya Kuma yi addu\’ar Allah ya jikansa ya sa Aljanna ta zama makoma ya Kuma ba Majalisar Sarkin tare da Iyalan marigayin hakurin jure rashin.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here