An Kaddamar Da Kudin Akwati A Jigawa

0
861
  Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya kaddamar da kudin akwatuna da ke a kowace mazaba domin gudanar da wadansu muhimman ayyukan ci gaban jama\’a.
Kamar yadda tashar talbijin ta NTA ta dauko kai tsaye a lokacin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai Jihar ta kwanaki biyu domin bude wadansu muhimman ayyukan da Gwamnatin jihar ta kammala a wurare daban daban.
An ji Gwamna Badaru Abubakar na bayani a wurin taron rana ta biyu da aka yi a dandalin taro na Malam Aminu Kano da ke birnin Dutse.
Badaru Abubakar ya bayyana cewa abin da suka zo yi a wannan dandalin taro sun zo ne domin kaddamar da kudin akwati da za a rika ba kowane akwati a dukkan mazaba akalla naira dubu hamsin ko dari domin gudanar da wasu ayyukan da jama\’a za su amfana, amma kuma idan an bar su lamarin zai zama wata matsala daban.
\”Za mu rika aiwatar da ayyuka irin na taimaka wa mata masu haihuwa, ginin rijiya ko gyaran burtsatse da za ka ga naira bai fi dubu sha biyar ba amma yana neman zama wata matsala daban, suka za a yi amfani da wannan kudin akwati a aiwatar da su da nufin warware matsalar da ke zagaye da akwatuna.
Badaru ya kara da cewa suna koyi ne da abin da Gwamnatin Tarayya ke yi karkashin Buhari na cika alkawarin ba mutane dubu biyar biyar a mazaba wanda hakan na taimakawa kwarai.
Gwamnan ya tunatar da jama\’a wani taken da yake cewa ba kashe zomon ba sai jama\’a su ce rataya aka ba shi, wato dai magana ce kowa ya san inda batun ya dosa.
Ya kuma shaida wa shugaban kasa da \’yan tawagarsa cewa akwai kungiyoyi da sauran jama\’ar da suke son yi wa Gwamnatin Tarayya karkashin Buhari Godiya bisa irin abubuwan da aka aiwatar masu na jin dadi wato kamar \’yan kungiyar noman shinkafa da dai jama\’a da dama amma saboda wata hidimar da shugaban yake da ita ba za a samu damar yin hakan ba amma shi ya isar da sakonsu baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wurin taron shugaba Muhammadu Buhari cewa ya yi ba zai ci amanar jama\’a ba kuma da saninsa ba za a ci amanar kowa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here