Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Ta\’aziyyar Isyaka Rabi\’u  

0
659
 Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari Dalkatun Katsina tare da tawagarsa sun kai ziyarar gaisuwar ta\’aziyya gidan Marigayi Shaikh Isyaka Rabi\’u shugaban darikar Tijjaniyya a Afrika.
Sun dai kai wannan gaisuwar ne a gidan marigayin da ke Gwauron Dutse cikin garin Kano
Gwamnan Jihar Katsina ya samu kyakkyawar maraba daga wasu \’ya\’yan marigayin bisa jagorancin Babban dan marigayin Alhaji Nafi\’u Isyaka Rabi\’u, wanda shi ne Manajan Daraktan rukunin kamfanin Isyaka Rabi\’u .
 Sauran \’ya\’yan da suka karbi Gwamna Masari da tawagarsa sun hada da Alhaji Abdussamadu Isyaka Rabi\’u, Manajan Daraktan kamfanin BUA da kuma Alhaji Rabi\’u Isyaka Rabi\’u da ake kiransa da sunan Alhaji karami, Manajan Daraktan kamfanin jiragen sama na IRS.
Masari ya yi addu\’ar Allah ya ba marigayin gidan Aljanna Firdausi bisa duba da irin yadda marigayin ya yi aikin yada addinin musulunci a duk tsawon rayuwarsa baki daya.
 Da yake jawabi a madadin iyalan Alhaji Nafi\’u Isyaka Rabi\’u addu\’ar Allah ya saka wa Gwamna ya yi bisa kokarin zuwa ya yi masu ta\’aziyya duk da irin ayyukan da Gwamnan yake da su amma ya kawo masu gaisuwa, hakika mun gode Allah ya saka da alkairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here