WANI matashi da ba a bayyana sunan a ba ya haye kan kololuwar hasumiyar masallacin juma’a na unguwar Ja’en da ke kan titin Sharada a garin Kano.
Maigadin masallacin, Mallam Adda’u, ya bayyana cewar matashin ya karya wata taga ne kafin ya samu damar shiga masallacin kuma duk da sun yi kokarin dakatar da matashin hakan ba ta yiwu ba.
Sannan ya kara da cewa, matashin ya ce ba zai sauko ba saboda wasu na neman shi za su kashe shi, duk da bai bayyana ko su wane ne ba.
Wani daga cikin ‘yan kwamitin masallacin, Malam Kabiru, ya ce sun sanar da jami’an ‘yan sanda bayan samun matashin cikin hasumiyar.
Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar sauko da matashin tare da tafiya da shi ofishinsu domin zurfafa bincike a kansa.
Bisa ga dukkan alamu matasan jihar Kano sun samo wani sabon salon hayewa kan gini ko karafa masu tsayi duk lokacin da suke da bukatar nuna fushi ko damuwarsu.