ZA MU RABA WA \’YAN NAJERIYA KUDADEN DA ABACHA YA DIBA – Inji Shugaba Buhari

0
913
Shugaba Muhammadu Buhari
Daga Usman Nasidi

A ranar Litinin, 14 ga watan Mayu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta rarraba wa \’yan Najeriya Dala Miliyan 320 wanda Abacha ya sata ya boye a kasashen ketare a lokacin da yake shugabancin kasa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a taron kara wa juna sani na kasashen rainon Ingila reshen Afirka a kan yaki da cin hanci da rashawa da ke gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo ya bayyana cewa wannan shi ne sharadin da kasar Switzerland ta bayar yayin da take danka kudin ga Najeriya.

A halin da ake ciki yanzu kuma wani rahoto na bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sayar wa ‘yan kasuwa da wani bangare na kamfanin tatar mai na Najeriya (NNPC), idan har ya zama shugaban kasa.

Atiku yayi bayanin cewa kamfanin na NNPC ya dade a cikin matsalar rashin kulawa a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here