AZUMIN WATAN RAMADAN DA FALALARSA

0
1277
Sheikh Muhammad Sulaiman Adam. Babban Limamin Masallacin Sultan Bello Kaduna
AZUMIN WATAN RAMADAN DA FALALARSA
HUDUBAR SHEIKH MUHAMMAD SULAIMAN ADAM
BABBAN LIMAMIN MASALLACIN SULTAN BELLO DA KE KADUNA
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, mai girma da buwaya tsira
da amincin Allah su kara tabbata ga Annabin tsira, Annabi Muhammad SAW
da alayensa da sahabansa da matayensa, da duk wanda ya yi koyi da shi
har zuwa tashin alkiyama.
Bayan haka ya ‘yan uwa masulmi, ina yiwa kaina wasici da kuma ku, kan
muji tsoran Allah a cikin dukkan al’amuran da zamu yi.
Allah mazaukakin sarki yana cewa yaku wadanda kuka yi imani, an
wajabta maku Azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka zo kafinku,
ana fatar kuji tsoran Allah.
Ya ‘yan uwa masu  albarka, ya zama wajibi ga musulmi kada yayi sakaci
a lokacin da Allah mazaukakin sarki ya bashi dama. Kada ya yi wasa da
wannan damar. A lokacin da zai sami dama ya yi ibada. Lallai mu
zamanto masu rige rige wajen aikata ayyukan alheri.
Allah mazaukakin sarki ya kwadaitar damu, mu yi rige rige wajen
alheri. Yana cewa  kan haka ne masu tsare su zuba tsere suyi rage rige
wajen aikin alheri.
Haka Allah yake cewa ku yi gaggawa wajen neman gafarar ubangijinku, ku
yi gaggawa wajen neman aljannah da fadinta ya kai fadin  sammai da
kassai gabaki daya. An tanadeta ga masu takawa,  tana nan tana
jiranku.
Ya ku ‘yan uwa masu tsoran Allah, Allah madaukakin sarki ya fifita
abubuwa a kan abubuwa, mutane a kan mutane lokaci a kan lokaci zamani
a kan zamani, kowanne abu akwai fifiko a tsakani. Saboda haka wannan
falalace. Daga lokutan da aka fifita akwai lokacin watan Azumin
Radaman.
Ya ‘yan uwa masu albarkar ga wannan lokaci na watan Azumin Ramadan ya
zo, wannan wata ne mai albarka wata ne wanda yake zama kamar rana ce a
cikin taurari.  Wata ne da Allah madaukakin sarki ya saukar da
Alkura’ani a cikinsa.
Allah yana cewa watan Azumin Ramadan wanda aka saukar da Alkura’ani a
cikinsa, akwai shiriya  da kuma fayyace tsakanin gaskiya da karya.
‘Yan uwa masu albarka wannan wata ne da Allah ya wajabta mana Azumi ba
mu kadai ba, ya wajabtawa duk halittun da suka zo kafinmu. Allah
madaukakin sarki ya wajabta masu yin Azumi. Amma yaya suke yi wannan
bai shafe mu ba.
Wannan wata ne na tuba, wata ne na gafara wata ne da yake kankarewa
mutane zunubai. Hadisin Abu Huraira yana cewa manzon Allah SAW ya ce a
sallar biyar, wato tsakanin sallah zuwa tsakanin juma’a zuwa juma’a
tsakanin Ramadan zuwa Ramadan ana gafartawa mutum. Wallahi banda
musulmi babu wanda yake samun wannan garabasar. Ace tsakanin sallah da
sallah duk abin da kayi, idan kazo kayi sallah an yafe maka. Tsakanin
juma’a zuwa juma’a idan kazo kayi an yafe maka, tsakanin Radaman zuwa
Ramadan abin da kayi an yafe maka, idan ka nisanci miyagun ayyuka.
Babu shakka watan Azumi wata ne na  lada da gafara. Ke nan sai mu yi
koyi yadda Allah madaukakin sarki yake gafarta mana, yake yafe mana
muma mu yafewa ‘yan uwanmu wadanda suka yi mana laifi, basu sani ba.
Mu yafewa wadanda suka yi mana laifi da saninsu. Mu yafewa wadanda
suka yi mana laifi bisa kuskure.  Domin da wannan ne zaka zamanto
fintinkau a ranar tashin alkiyama, a gaban sauran halittu.
Idan zaka sami wanda ya saba maka ka fada masa kace saboda falalar
wannan wata na Ramadan, na yafe maka laifin da kayi mani har abada.
Idan da musulmai zasu yi haka, da mun tashi daga matsayinmu na
musulmai mun fara komawa matakin zama mumunai. Amma har yanzu muna nan
a musulmanmu. Saboda idan an yi maka laifi zaka ce sai ka rama. To bai
kamata ba, ya kamata mu yi koyi da wannan koyarwa da Allah madaukakin
sarki ya sanya mana. Domin watan Azumi an sanya shi ne don ya koyar da
mu irin wadannan abubuwa. Kada ka damu da girman laifin da aka yi
maka, ka dubi girman wanda zaka yafewa domin shi. Kada ka damu da
girman laifin da aka yi maka.  Idan  aka yi maka laifi komai girmansa
ka kalli girman Allah ka yafewa wanda ya yi maka wannan laifi.
Allah yana cewa shin ku bakwa son Allah ya yafe maku?  Idan aka yiwa
mutum  laifi ya yafe, zai ga irin sakamakon da Allah zai bashi.
Saboda haka jama’a ku yi yafiya tsakaninku da ‘yayanku, tsakaninku da
matayenku  tsakaninku da abokanan sana’arku  tsakaninku da abokan
huldarku ku yafe masu.
Allah ka sheda duk wanda ya sheda ya yi mani wani abu ni dai na yafe
masa. Ko na sani ko ban sani ba. Har wadanda suke cin namana. Kuma ina
rokon Allah ya gafarta masu.
Saboda haka manzon Allah SAW ya bayyana mana cewa duk mutumin da ya
tashi ya yi Azumin watan Ramadan yana neman yardar Allah da ikon Allah
ya yarda da Allah ne ya yi masa umarni, yana neman ladan Allah ya
yarda zai bashi lada. Allah madaukin sarki ya ce za a yaye masa
zunubansa gabaki daya.
Idan watan Azumi ya kusa ma’aiki SAW  cewa yake yi, ya kai mai neman
alheri,  zo ga alheri nan yazo maka. Ya kai mai neman  shirri an
durkusar da kai, an dakatar da kai a kan wannan shirri naka. Sannan
yake cewa Allah yana da wadanda yake yantawa daga cikin wuta. Wannan
kowanne dare na Radamadan ne. Allah kasa dukkan bayinka wadanda suka
zo wannan sallah da wadanda basu zo ba, Allah kasa muna daga cikin
wadanda za a yantar.
Wannan wata ne na albarka wata ne da ake bude kofofin aljannah ake
rufe kofofin wuta ake daure kangagararrun shedanu. Allah ka bude mana
kofofin Aljannah.
Wata ne na hakuri, hakuri kuma yana bayyana ne balo balo. Domin
hakurin ne zai hana mutum ci da sha da kallon abin da kake son ka
kalla da jin abin da kake son kaji na wake wake, amma a wannan lokaci
na watan Azumi zaka hakura ka bar wadannan abubuwa. Hakuri kuma bashi
da sakamako sai gidan Aljannah.
Allah yana cewa zai cikawa wadanda suka yi hakuri ladansu batare da ya
yi masu hisabi ba, Allah kasa muna ciki. Watan Azumi wata ne na addu’a
domin addu’a tana karbuwa a lokacin Azumin wata Ramadan, shi yasa
Allah madaukakin sarki da ya yi maganar ayoyin Alkura’ani kan Azumi.
Daga karshe  sai ya kawo cewa idan bayina suka tambaye ka dangane da
ni tofa ina kusa. Saboda haka Allah madaukaki yana jinka yana ganinka,
tambaye shi abin da zaka tambaye shi zai baka. Saboda haka, mu dage
muyi ta yin addu’o’i a wannan lokaci na wata Azumin Ramadan.
Bayan haka wata ne na baiwa da kyauta da kuma kare kai daga abubuwan
da basu da kyau.
‘Yan kasuwa watan da zaku sami alheri ke nan. Watan da zaku yiwa
jama’a sauki, ku sayar masu da kayayyaki da sauki domin su sami damar
jin dadin bauwata Allah su sami lada, kuma ku sami lada.
Sa’annan duk abin da kasan kana aikatawa na haram ka bar shi, don kar
ya zama kayi aikin banza kana Azumi ana daukar ladan ana baiwa wadanda
kake cuta, don haka jama’a a kiyaye da wannan.
A nan zan yi amfani da wannan dama nayi kira ga al’ummar musulmi kan
mu yi amfani da wannan wata na Azumi muyi ta rokon Allah, masifar nan
da take ta damunmu musamman a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna da jihar
Zamfara da jihar Taraba Allah ya yaye mana. Domin wannan masifa  ta
shafemu gabaki daya. Babu abin da zai fitar damu daga cikin wannan
masifa sai addu’o’i saboda haka muyi amfani da wannan dama mu yi
addu’o’i Allah ya yaye mana wannan masifa.
Sa’annan watan Azumin nan yazo ga siyasa ta tunkaro, babu abin da zai
cire mu daga masifar tashe tashen hankulan siyasa  illa addu’a. Don
haka mu tsaya, mu yi addu’a mu roki Allah madaukakin sarki ya zaba
mana abin da yafi alheri. Kada mu ce ga abin da muke so, idan muka ce
ga abin da muke so, Allah zai kyale mu da abin da muke so. Amma idan
muka yi addu’a Allah ya zaba mana mafi alheri, muka tsaya muka yi aiki
ba dare ba rana, sai Allah ya kawo mana wanda yake alheri.
Kuma idan Allah ya kawo shi to muyi hakuri da yadda zamu sami kanmu.
Har’ila yau ina son nayi amfani da wannan dama wajen yin bayani kan
abubuwan da zamu yi a wannan masallaci na Sultan Bello, a wannan
lokaci na watan Azumin Ramadan.
Gyara ne zamu yi,  zamu tsananta tsaro a wannan masallaci, masu ababen
hawa wuraren da zasu zauna daban. Wararen masu mashina daban.  Mun
tanadi ‘yan agaji da jami’an tsaro na wannan masallaci. Kuma zamu kara
dauko jami’an tsaro daga waje wadanda zasu taimaka mana wajen tabbatar
da tsaro a wannan masallaci. Babu wani mai kayan sayarwa da za a bari
ya shigo cikin harabar wannan masallaci. Masu sayar da kaya suje can
waje su sayar da kayayyakinsu. Don Allah jama’a su bamu hadin kai kan
wannan mataki da muka xauka.
Bayan haka ina amfani da wannan dama, wajen sanar da jama’a cewa mun
sanya wata na’ura a wannan masallaci, wadda za iya ganin  wannan
huduba  a ko’ina a duniya, a lokacin da ake gabatar da ita. Kuma zamu
sanya na’urori na tsaro a wannan masallaci don tabbatar da tsaro a
wannan masallaci.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here