HUKUMAR ALHAZAN FILATO BA ZATA AMINCE A SAYAR DA KUJERUN GWAMNATI BA

0
710
Barista Auwal Abdullahi Sakataren hukumar jin daxin alhazai ta jihar Filato,,,
Isah Ahmed, Jos
BABBAN sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Filato, Barista
Auwal Abdullahi ya bayyana cewa a bana hukumar jin dadin alhazai ta
jihar Filato ba za ta amince a sayar da kujerun gwamnati da aka bai wa
jama’a ba. Barista Auwal Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacin da
yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.
Ya ce suna samun labarin cewa  wadansu maniyyata  suna jiran kujerun
gwamnati ne saboda sun fi sauki, don haka basu zuwa da wuri suna biyan
kudaden kujerun aikin hajjinsu.
Ya ce muna  sanar da jama’a  cewa  bana ba za a sayar da wata kujerar
gwamnati ba a jihar Filato. Idan ma da ana yi, to bana hukumar alhazan
jihar Filato, ba za ta amince ba. Domin idan aka sayar da kujerun da
gwamnati ta bayar,  manufar bayar da kujerun gwamnati bai yuwu ba.
Sakataren hukumar alhazan ya yi bayanin cewa sam bai da ce ba, ace
gwamnati ta ware kujeru a baiwa bayin Allah, su tafi aikin hajji sai
wasu wadanda basu da alaka da aikin hajjin, su karbi wadannan kujerun
suje su sayar a wulakance.
‘’Don haka bana ba zamu amince ba. Zamu yi iyakar kokarinmu  muga cewa
duk wanda aka bashi kujerar gwamnati, ya karbi  kujerar kuma ya tafi
aikin hajjin’’.
Barista Auwal ya ce a yan kwanakin nan sun je  lasa mai tsarki,  kan
maganar  masaukan alhazan jihar Filato da kuma wadanda zasu dafa masu
abinci a lokacin aikin hajjin bana, da maganar zaman arfa da muzulifa
a lokacin aikin hajji. Kuma sun  sami kwararrun kamfanoni kan wannan
aiki da wuraren saukar alhazai masu kyau.
Ya ce har yanzu ba a yanke kudin aikin hajjin bana ba, amma in Allah
ya yarda ana sa ran za a rage kudin aikin hajjin bana, kasa da na
shekarar da ta gabata.
Ya ce har yanzu mutane basa fitowa yadda ya kamata wajen biyan kudaden
kujerun aikin hajjin bana a jihar Filato.
Don haka ya yi kira ga alhazan da suka ajiye kudadensu  su hanzarta
zuwa su cika kudadensu, wadanda kuma suna da niyya basu bada komai ba,
su hanzarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here