KUNGIYAR BILMPAN ZA TA YI AIKIN TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA TSAKANIN MAKIYAYA DA MANOMA-Ali Rimin Dako.

0
742
Alhaji Ali Rimin Dako shugaban kungiyar
JABIRU A HASSAN,  Daga Kano.
SHUGABAN gamayyar kungiyoyin fulani makiyaya ta ( BILMPAN ) na kasa Alhaji Ali Muhammad Rimin Dako ya ce kungiyarsu tana gudanar da shirye-shirye na bunkasa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin fulani makiyaya da manoma a sassan Nahiyar Afirka musamman  a daidai wannan lokaci na rikice-rikice tsakanin bangarorin biyu.
Ya yi wannan albishir ne a zatawar su da wakilinmu  a ofishinsa, inda kuma ya nunar da cewa daukar matakai cikin tsari zai taimaka sosai waje rage yawaitar rigngimu tsakanin manoma da fulani makiyaya,sannan hakan zai taimaka wajen samar da ingantacciyar masalaha tsakanin wadannan muhimman bangarori biyu cikin nasara.
Alhaji Ali Rimin Dako ya kuma bayyana cewa kungiyar ta BILMPAN  tana aiki a sassa daban-daban na Nahiyar Afirka, sannan tana da cikakkiyar dangantakar aiki tsakann ta da sauran kungiyoyi na fulani makiyaya wadanda suke taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da kaunar juna  da kuma hadin kan makiyaya bisa yin la\’akari da bukatun kowace al\’umma.
Haka kuma shugaban ya yi amfani da wannan dama wajen yn kira ga mahukumta na msauran kasashen dake Nahiyar Afirka da su gaggauta fara daukar matakai na magance aukuwar rikice-rikice tsakanin fulani makiyaya da manoma, tare da kakkafa makarantu na \’ya\’yan makiyaya domin su kara  samun  ilimin addini da na zamani ta yadda zamantakewar su za ta inganta a dukkan inda suke zaune.
Sannan ya gode wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen bunkasa ilimin \’ya\’yan makiyaya a fadin jihar  wanda hakan ta sanya \’ya\’yan makiyaya a jhar suke samun ilimi na addini da na zamani, tare da fatar cewa gwamnan zai kafa wata hukuma  mai zaman kanta wadda za ta kula da sashen ilimin \’ya\’yan makiyaya a jihar ta Kano.
A karahe, Alhaji Ali Muhammad Rimin Dako ya yaba wa fulani makiyaya da manoman wannan kasa tamu saboda kokarin da suke yi  wajen tabbatar da ganin tattalin arzikin kasarnan yana kara bunkasa ta fannoni daban-daban, sannan ya yi fatar cewa nan gaba kadan za\’a kawar da  dukkanin wani sabani dake tsakanin bangarorin biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here