KUNGIYAR IZALA TA TURA MALAMAI 520 DON GUDANAR DA TAFSIRIN AZUMIN AZUMIN WATAN RAMADAN

0
1649
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir lokacin da yake bude tafsirin da yake gabatarwa a garin Jos
Isah Ahmed, Jos
KUNGIYAR Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, ta tura
malamai masu tafsiri guda 520 zuwa jihohi daban daban na tarayyar
Nijeriya da kasashe daban daban, don gudanar da tafsirin Azumin watan
Ramadan da aka fara. Shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka, a lokacin da
yake bude tafsirin Azumin watan Ramadan da yake gabatarwa a garin Jos,
babban birnin jihar Filato.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya ci gaba da cewa a bana, sun tura malamai
masu  tafsiri guda 520  daga ofishinsu na kasa, zuwa jihohi daban
daban na tarayyar Nijeriya da qasashe daban daban don su je su gudanar
da tafsirin Azumin watan Ramadan, kamar yadda aka saba yi a kowace
shekara.
Ya ce  a cikin malaman da aka tura  har da  Sheikh Ahmed Imam  wanda
zai je ya gabatar  da tafsiri a birni New York da ke kasar Amerika.
Har’ila yau ya ce an tura  malamai masu tafsiri  zuwa kasashen  Sudan
da  Nijar da Kamaru da Togo da Ghana da Chadi Afrika ta tsakiya da
dai sauransu.
Haka kuma ya ce rassan  kungiyar na jihohi da kananan hukumomi, suma
sun  tura nasu malaman  masu tafsiran zuwa wurare daban daban don
gudanar da tafsirin Azumin na watan Ramadan.
Sheikh  Jingir ya yi bayanin cewa wannan wata ne na ibada, saboda an
daure shedanu a wannan wata. Don haka ya yi kira ga  jama’ar musulmi
su rike karatun Alkura’ani da salloli  da ciyar  marayu da marasa
galihu maza da mata  a wannan wata.
Har’ila yau ya yi kira ga ‘yan kasuwa su ji tsoron Allah, su saukaka
farashin kayayyakin masarufi a wannan wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here