Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN kungiyar kwadago ta jihar Filato Kwamared Jibrin Bancir ya
bayyana cewa yanzu ma’aikatan jihar Filato ba su da wata matsala wajen
biyan albashi. Kwamared Jibrin Bancir ya bayyana haka ne a lokacin da
yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce yanzu babu abin da zamu cewa gwamnatin Filato dangane da biyan
albashin ma’aikata sai dai mu yi godiya ga Allah. Musamman idan muka
duba irin wahalhalun da ma’aikatan jihar Filato suka sha a baya kan
biyan albashi.
Ya ce domin a zamanin gwamnatin da ta gabata, sai da ma’aikatan jihar
Filato suka yi watanni 8 ba a biya su albashi ba. ‘Yan fansho kuma
sai da suka yi watanni 12 ba a biya su ‘yan fansho ba.
Ya ce babu shakka a wancan lokaci ma’aikata da sauran jama’ar jihar
Filato sun wahala, sakamakon wannan rashin biyan albashi. A lokacin
wasu sun rasu saboda wahala, sakamakon rashin biyan albashi.
‘’Amma da Allah ya kawo wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad
Buhari da gwamnatin Filato ta Simon Lalong kudin tallafin da shugaba
Buhari ya baiwa jihohi, gwamna Lalong ya nada kwamiti aka biya
ma’aikata hakkokin da suke bi. Haka kuma da aka baiwa gwamna Lalong
kudaden Paris Club aka biya ‘yan fansho dukkan kudaden da suke bi’’.
Kwamared Bancir ya yi bayanin cewa yanzu duk ma’aikacin gwamnatin
jihar Filato ko ma’aikacin qaramar hukuma a jihar Filato, idan ka
tambashi kan maganar biyan albashi, zai tabbatar maka cewa yana samun
albashinsa kafin karshen wata, wani lokaci ana biyan albashi a kwanaki
27 ko 26.
Ya yi kira ma’aikatan jihar Filato su baiwa wannan gwamnati goyan
baya da hadin kai, musamman kan kokarin da take yi wajen biyan
ma’aikata kudaden albashinsu a kan lokaci.
Dolene major hamza almustapha yaji kunya saboda baishirya yaki da buhari ba Allah yakaimu zaben 2019.