ALLAH YA YI WA SHUGABAN KAMFANIN JARIDAR NNN/GTK RASUWA

0
638
Marigayi Malam Tukur Abdurrahman MD, NNN
Daga Usman Nasidi
Inna lillahi Wa Inna Ilaihi Raju\’un!!!
Allah Ya yi wa Shugaban Kamfanin Jaridar New Nigerian Newspapers Limited da Gaskiya Ta Fi Kwabo, Alhaji Tukur Abdulrahman rasuwa a daren jiya Alhamis.
Marigayi Tukur ya rasu ne a wani asibitin H2 Speciality Clinic da ke Asokoro a garin Abuja bayan wata \’yar gajeruwàr rashin lafiya da ya yi fama da ita na wasu \’yan kwanaki, bayan samun saukin da jikinsa ya yi daga dadadden ciwon da ya same shi kimanin fiye da shekara daya kenan.
Marigayin dan shekaru 57 da haihuwa, ya rasu ya bar mata daya da yara biyar a garin Kaduna, kana za a yi jana\’izarsa a yau Juma\’a da misalin karfe 4 na yammah a garin Daura ta Jihar katsina.
Alhaji Tukur, an haife shi ne a ranar 12 ga watan Disamba, 1960 kana ya yi karatun firamarensa a garin Daura sannan ya yi sakandare a kwalejin gwamnati ta garin Kaduna, kamin ya je jami\’ar Bayero inda ya yi karatunsa na jami\’a.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya yi aiki a karkashin sashen Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta New Nigerian Newspaper inda har ya kai matsayin  Editan ta, kana ya koma sashen turancin inda ya yi aiki a matsayin Edita na wani lokaci kafin ya zama shugaban kamfanin gidan Jaridar har zuwa karshen rayuwarsa.
Ubangiji Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kana Ya ba iyalensa, \’yan uwansa da abokan aikinsa hakurin jure wannan babbar rashin da muka yi, kana Ya sa mu cika da kyau da imani, ameen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here