Daga Usman Nasidi Kaduna
A ci gaba kokarin da gwamnatin Jihar Kaduna take yi don ganin ta inganta rayuka da al’ummar Jihar Kaduna, wata kungiyar Azama da wayar da kan al’umma wato (Rigasa Action And Awareness Forum RAAF) da ke garin Rigasa Kaduna ta jinjina wa Gwamna Nasiru El-Rufa’i bisa ga kokarin da yake yi don ganin ya inganta rayukan al’ummar gundumar.
Shugaban kungiyar Akitet Abubakar Rabiu Abubakar ne ya bayyana hakan a wata zantawarsa da wakilinmu a garin Rigasa, inda ya bayyana cewa gwamnatin Jihar na matukar kokari ta fannin raya birane da karkara, musamman gundumar Rigasa wanda a halin yanzu aka sake bada kwangiyar gyaran wata hanyar a cikin ta.
Ya ce “kasantuwar ziyarar da gwamnan ya yi don halartar wani taron karrama wasu al’ummar yankin da kungiyar ta gudanar a ranar litinin din data gabata, Gwamnan ya sake bada kwangilar gyaran Titin Makarfi Road wanda yake da mahada da babbar hanyar zariya, wanda shi ma ake kan gyaran shi a halin yanzu.”
A cewarsa, wasu daga cikin aiyukan da gwamnatin ta yiwa garin Rigasa sun hada Gyaran Babban Asibitin garin da sanya na’urori na zamani, Gina wasu azuzuwa da gyaran wasu makarantu, Gina Tagwayin hanya na Titin Zariya, mayar da Kasuwar garin izuwa na zamani, Samar da manyan aiyukan gwamnati ga al’ummar yankin, gyaran kananan asibitocin kiwon lafiya, biyan hakkin mutanen da aikin Tagwayen hanyar ya shafa, da yin wasu abubuwa da dama wadanda basu iya misiltuwa.
Akitet Abubakar ya kara da cewa wannan karamci da nuna kauna da Gwamnan yake mawa al’ummar gundumar, a gaskiya ba su taba zaton za a samu wata gwamnati wacce zata kawo musu cigaba irin wannan ba, domin tayi musu aiyuka da dama kuma har yanzu tana kanyi, don haka ya zama wajibi ne su godewa wannan gwamnatin ta Malam Nasiru El’Rufa’i.
A karshe, Shugaban ya roki gwamnatin Jihar da ta taimaka ta sanya hanyar Abuja Road tun daga Titin Zariya Road har izuwa gadar Hayin Malam Bello a cikin aiyukan da take yi, domin hanyar tana cikin wani mummunar yanayi wanda jama’a da dama ke kokawa da ita musamman a yanzu da damuna ta kama.