Isah Ahmed, Jos
KUNGIYAR ‘yan Nijar mazauna Nijeriya na yankin jihohin arewacin Nijeriya, sun bukaci gwamnatin kasar Nijar, ta sanya baki wajen ganin an gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar ‘yan Nijar mazauna Nijeriya. Kungiyar ta bayyana wannan bukata ce, bayan kammala taron da suka gudanar a garin Jos babban birnin jihar Filato, a karshen makon da ya gabata.
Da suke bayyana matsayar kungiyar a madadin ‘yan kungiyar, a wajen wannan taro da ya sami halartar jihohi 13 da ke arewacin Nijeriya, sakataren kungiyar ‘yan Nijar mazauna jihar Filato Alhaji Abubakar Sadik Muhammad da jami’in hulda da jama’a na kungiyar ta jihar Filato Alhaji Muhammad Usman da Mai kula da sha’anin tsaro na kungiyar reshen jihar Filato Alhaji Muhammad Danlami Sulaiman, sun bayyana cewa tun lokacin tsohon shugaban kungiyar ta ‘yan Nijar mazauna Nijeriya marigayi Alhaji Ibrahim Sarkin Malamai ya rasu, shekaru 13 da suka gabata, aka bayar da rikon shugabancin kungiyar. Amma har ya zuwa yau, ba a kira mutane don gabatar da zaben sababbin shugabannin kungiyar ba.
Suka cigaba da cewa a ka’idar kungiyar shekaru biyu ake bayar da rikon shugabancin kungiyar. Amma yau shekaru 13 ke nan ba a yi zaben sababbin shugabannin wannan kungiya ba, tana nan a hanun masu riko.
Suka ce wadanda suke rikon wannan kungiya wadansu tsurarun mutane ne, kuma suna raba kan ‘yan kungiyar don cumma burinsu.
‘’Don haka wannan taro ya nuna rashin amincewa da wannan riko da suke yi. Don haka taron ya yi kira ga gwamnatin kasar Nijar ta sanya baki, domin a sami shugabanci mai inganci a wannan kungiya, ta ‘yan Nijar mazauna Nijeriya, ta hanyar gudanar da zabe’’.
Har’ila yau taron ya yi kira ga ‘yan Nijar mazauna Nijeriya su hada kansu, su zauna lafiya kuma su guji shiga kungiyoyin ta’addanci da gwamnatocin Nijeriya da Nijar suka haramta kamar kungiyar boko haram.
Haka kuma taron ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijar mazauna Nijeriya, su bi dokokin da kungiyar kasashen Afrika ta yamma ta sanya. Musamman mallakar takardun da dokokin kasashe suka sanya da kuma mallakar takardar zama a kasa.