GASKIYAR BUHARI CE TA SANYA ‘YAN NIJERIYA  SUKA  AMINCE  DA  SHI-SHEIKH SA’IDU JINGIR

0
1054
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

 Isah Ahmed, Jos

SA\’I na kasa kuma mataimakin  shugaban majalisar malamai na kasa na biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir  ya bayyana cewa gaskiyar shugaban kasa Muhammad Buhari ce, ta sanya ‘yan Nijeriya suka amince da shi kuma suke bada rayukansu a kansa. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen bude wani sabon masallacin juma’a da wani bawan Allah mai suna Alhaji Malami Muhammad Saminaka ya gina, a wata unguwa mai suna ganyen oda da ke garin Saminaka a jihar Kaduna, a ranar juma’ar da ta gabata.

Ya ce gaskiyar Buhari  ce ta sanya ‘yan Nijeriya suka amince da shi kuma suke bada rayuwarsu a kansa. Domin duniya ta yarda Buhari ba barawo ba ne.

‘’Rashin sa’ar da aka yi a Nijeriya, ita ce miyagun fadawa ne  suka  kewaye Buhari. Wadanda suke kewaye da Buhari suna yi masa zagon kasa. Wannan ita ce damuwarmu a Nijeriya  yanzu. Mafiya yawan  masu cewar sune ‘yan Buhari ba da gaske suke yi ba, domin da gaskiya ne, da yanzu an sami gagarumar nasara a Nijeriya. Amma duk da haka mu mun ga amfanin mulkin Buhari, don haka ba zamu yarda miyagun abubuwan da suka faru a baya, na tashe tashen hankula da  zubar da jini su sake dawowa a Nijeriya  ba’’.

Sheikh Sa’idu Jingir ya gargadi al’ummar Nijeriya  su yi hattara da hayaniyar ‘yan siyasa da ke faruwa yanzu a Nijeriya.  ‘Yan Nijeriya kada ku yarda ‘yan siyasa su sanya ku a cikin wannan hayaniya da suke  ta yi, ta  hanyar sanya ku  gaba da juna.

Ya yi kira ga al’ummar musulmin Nijeriya su hada kai, su guji sanya kabilanci a tsakaninsu.

Ya ce addinin musulunci na dukkan kabilun duniya ne,  ba na wata kabila kadai ba. Don haka musulmi ku daina yin kabilanci a tsakaninku.

Ya yaba wa Alhaji Malami Saminaka kan wannan sabon masallacin juma’a da ya gina. Ya ce wannan bawan Allah ya shafe sama da shekara 40, yana gwagwarmayar taimakawa  addinin musulunci. Don haka ya yi kira ga al’ummar musulmi suyi koyi da shi.

A nasa jawbin daraktan cibiyar bunkasa al’umma ta Alhuffaazh da ke garin Saminaka Dokta Muhyiddeen Ibrahim Salahuddeen  ya yi kira ga al’ummar garin Saminaka  su cigaba da  zaman lafiya da junansu.

Ya yi fatar Allah yasa wannan masallaci ya zamanto hadin kan al’ummar musulmin Saminaka da kasa  gabaki daya.

Daga nan ya yi addu’ar Allah ya sakawa wanda ya gina wannan masallaci da alheri.

Tun da farko a nasa jawabin Sarkin unguwar Gayen oda da ke garin Saminaka, da aka gina wannan masallaci kuma daya daga cikin ‘yayan Alhaji Malami Saminaka,  Alhaji Hassan Malami Muhammad ya bayyana cewa abin da ya karfafawa mahaifinsu gwiwar gina wannan masallaci, shi ne domin amfanar da al’ummar wannan unguwa gabaki daya.

Ya cewa wannan masallaci ba shi ne mahaifin nasu ya fara ginawa ba. Domin ya zuwa yanzu ya gina masallatai sama da guda 10 da makarantu guda 2 a cikin garin Saminaka da kewaye.

Ya yi  kira ga al’ummar wannan unguwa  su taru su raya wannan masallaci, ta hanyar zuwa suna yin salloli tare da saurararon karatuttukan da za a rika gabatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here