An Sace Matar Kwamishina Da ‘Ya’yansa Uku A Zamfara

0
609
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Mustapha Imrana Abdullahi

WADANSU ‘yan  Bindiga da suka je gidan wani Kwamishina a Jihar Zamfara sun sace matar kwamishinan da ‘ya’yansa uku

Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana cewa maharan da ba a san ko su waye ba sun isa gidan Kwamishina Abdullahi Gurbin Bore ne da safe.

Kamar yadda wani wanda ya ga lamarin da idanunsu ya shaida wa majiyarmu cewa maharan sun je gidan inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi sai suka kutsa kai cikin gidan nan da nan suka dauke matarsa da ‘ya’yansu shida cikin mota

Kwamishinan ya tabbatar da sace iyalin nasa inda ya tabbatar wa majiyarmu cewa uku daga ciki ‘yan uwansa ne da matarsa da kuma ‘ya’yansa.

Ya ce maharan ba su tuntube shi ba balantana su nemi wata diyya.

\”Ba su nemi diyya daga wurinmu ba. Ba mu ma ko yi magana da su ba, amma dai mun kai wa jami\’an tsaro rahoton faruwar lamarin\”in ji Kwamishina.

Jihar Zamfara dai na daga cikin wuraren da suke da matsalar tsaro, inda masu satar mutane da barayin shanu ke kai hari a wurare daban-daban a jihar.

Jihar ta samu tsawon lokaci ana samun matsalolin kai hare-haren barayin shanu da ‘yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here