ANNOBA: CUTAR KWALARA TA HALLAKA MUTUM 1, TA KWANTAR DA 40 A KADUNA

0
684
Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna
Daga Usman Nasidi

AKALLA dalibai 40, arba’in ne aka garzaya da su asibiti da gaggawa cikin mawuyacin hali daga makarantar sakandarin gwamnati na \’yan mata da ke Kawo, jihar Kaduna, sakamakon barkewar annobar kwalara.

Majiyar ta samu labarin cewa wata daliba guda daya ta rigamu gidan gaskiya tun bayan barkewar annobar a cikin kwanakin karshen mako, kamar yadda jami’n dakile yaduwar cututtuka na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Ibrahim Suleiman ya tabbatar.

Jami’in ya ce akalla dalibai 89 cutar ta shafa, amma zuwa yanzu an magance ta daga jikin sama da rabin daliban, sai dai ya danganta bullar cutar ga yadda daliban ke yin bayan gida a wuraren da basu dace ba, dalilin da yasa ruwan makarantar ya gurbata kenan, ya janyo wannan bala’in.

Sai dai Daraktan lafiya na jihar Kaduna, Dakta Ado Zakari wanda ya kai ziyara makarantar ya ki bayyana adadin daliban da suka kamu da cutar, amma ya shawarce su a kan hanyoyin da za su bi wajen kauce ma kamuwa da ita.

Bugu da kari hukumar bada agajin gaggawa, Red Cross ta aika da jami’anta zuwa makarantar don wayar da musu kai a kan dabarun kauce ma kamuwa da kwalara da kuma hanyoyin tabbatar da tsafta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here