Babu Tsama Ko Rashin Jituwa A Tsakaninmu – Gwamnan Bauci

0
616
Shugaba Muhammadu Buhari

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNAN Jihar Bauchi Barista Muhammad Abubakar ya bayyana cewa babu wani sabani tsakaninsa da mataimakinsa Barista Nuhu Gidado da ya ajiye aikinsa don kashin kansa.

Gwamna Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta BBC .

Gwamnan ya ce duk masu bayanin cewa wai tsakaninsa da mataimakinsa ba su san abin da yake tsakaninsu ba ne ana yin shaci fadi ne kawai.

\” Ko shi da kansa Nuhu Gidado yana gaya wa mutane cewa babu wani mataimakin Gwamna da yake da gatan da shi yake da shi a cikin gwamnati, saboda ma\’aikatar da ta fi kowace ma\’aikata fadi da karbar kudi mai tsoka ta ilimi shi ne kwamishinanta ban da kasancewarsa mataimakin Gwamnan da ake tsare ka\’ida wajen mika masa ragamar mulki\”.

\” Ban taba yin tafiyar da ta kamata a mika wa mataimakin Gwamna ya rike mulki ban mika masa komai na mulkin kamar yadda doka ta tanadar ba\”.inji shi.

Gwamna Abubakar ya ce yana nan yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin zabo mataimakin Gwamnan da za a maye gurbinsa da Barista Nuhu Gidado da ya yi murabus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here