Gwamna Masari Zai Kammala Aikin Kasuwar Kasa Da Kasa Ta Dubai A Katsina

0
720
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
MAJALISAR zartaswa ta Jihar katsina ta tabbatar da shirin kammala kasuwar kasa da kasa ta Dubai da ke cikin garin Katsina
Kwamishinan kula da ma\’aikatar ayyuka da sufuri, Injiniya Tasi\’u Dandagoro ne ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartaswa na jihar karkashin jagorancin Gwaman Aminu Bello Masari a dakin taro na Gidan Gwnatin Jihar.  Injiniya Tasi\’u Doguru ya ce tuni aka amince da kamfanin Mess Multisystem a matsayin kamfanin kwararrun da zai rika duba aikin kammala kasuwar kasa da kasa ta Dubai.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa majalisar zartarwar ta tattauna a kan batun tun daga matakin ma\’aikata, da dukkan bangarorin Gwamnati da abin ya shafa karkashin tsarin APC na tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan al\’amura.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Masari ta himmatu wajen gina Tituna 71, inda ya ce wadansu daga cikin titunan sababbi ne wasu kuma ana cikin ayyukansu da kuma hanyoyin da bana kwalta ba guda 39 duk domin bunkasa rayuwar jama\’ar birni da karkara.
 Ya ce Majalisar zartarwar ta gamsu da irin yadda ayyukan hanyar ke tafiya a halin yanzu.
Da yake yi wa manema labarai jawabi mai ba Gwamnan shawara a kan harkokin ilimi mai zurfi Alhaji Bashir Ruwan godiya cewa ya yi majalisar zartarwar ta amince da wadansu Likitoci Takwas su ta fi domin samun horon kwarewa na zama kwararrun likitoci masu bayar da shawara har tsawon shekaru shida a kan fannoni daban-daban na kula da rayuwar dan Adam.
  Ya kuma bayar da tabbacin cewa a karshe idan sun samu horon dole za su Dawo ne Jihar Katsina domin su yi aiki a bangaren lafiya a jihar.
Taron manema labaran an yi shi ne karkashin jagorancin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida  na jihar Katsina Alhaji Hamza Muhammad Borodo, tare da rakiyar mai taimakawa Gwamna masari na musamman a kan harkokin yada labarai Alhaji AbdulBasir Labaran Malumfashi da mai taimaka wa Gwamna a kan harkokin Kafafen sadarwar yanar Gizo da dandalin sada zumunta  na zamani Alhaji Abdulhadi Ahmed Bawa Faskari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here