Daga Usman Nasidi
HUKUMAR \’yan sandan Najeriya tace har yanzu ba ta janye kiran da ta ke yi wa shugaban majalisar dattawa ba, Sanata Bukola Saraki, inda ta neme shi da ya bayyana a gabanta domin gabatar da bincike akan shi, kiran ya biyo bayan zargin da ake yiwa Sarakin da hannu akan harin da aka kai banki a garin Offa dake jihar Kwara ranar 5 ga watan Afrilu.
Hukumar \’yan sandan ta ce ita bata ba da sanarwar cewar ta janye kiran da take yi wa Sarakin ba, inda ta ce maganar cewar ta janye kiran na shi ba ta da makama, soki burutsu ne na \’yan jarida.
Hukumar \’yan sandan ta ce shugaban majalisar dattawan yana da tambayoyin da zai amsa a gaban ta, duk da dai hukumar tace har yanzu ba ta saka ranar karshe da ta ke neman shi ba, amma tabbas tana bukatar ya bayyana a gaban ta domin gabatar da bincike akan zargin da ake yi masa.
Jami\’in hulda da jama\’a na hukumar Mista Jimoh Moshood, shine ya sanar da hakan ga manema labarai jiya a babban birnin tarayya.
Kiran da ake yi wa Sarakin ya biyo bayan harin da wasu \’yan bindiga suka kai wani banki a garin Offa dake jihar Kwara inda suka kashe sama da mutane 30, da aka kama su suka nuna cewar Saraki ne da gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed suka saka su.
A amsar daya bayar game da tambayar da aka yi masa na cewa ko hukumar janye kiran da take yiwa Sarakin, Moshood yace: \”Wannan sanarwar ba daga wurin ta fito ba, kuma bamu da masaniya akan hakan.
\”Amma, kuma doka ta ce duk mutumin da aka kama da laifi to dole ne ya gabatar da kanshi a gaban hukumar \’yan sanda domin a gabatar da bincike akan shi, duk kuwa matsayin sa.
\”Mun gayyaci shugaban majalisar dattawan daya bayyana a gaban mu domin gabatar da bincike akan shi, sannan kuma ya kare kanshi akan zargin da ake yi masa.
Ya kara da cewa, \”Har yanzu hukumar \’yan sanda tana kan bincike akan shugaban majalisar dattawan, Sanata Bukola Saraki, kuma hukumar \’yan sanda zata yi iya bakin kokarin ta wurin ganin tatabbatar da gaskiya akan wannan lamarin.\”
Sannan hukumar \’yan sandan tace ta kara kama wasu mutane biyu wanda suke da hannu akan harin da aka kai garin na Offa.