Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta ba da belin tsohon gwamnan jihar Alhaji Mukhtar Ramalan Yero.
A ranar Alhamis da ta gabata ne kotun ta ba da umarnin tsare tsohon gwamnan a gidan yari bayan da Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da shi a gaban kotun.
Ana tuhumar tsohon gwamnan ne da laifuka hudu da suka hada da halatta kudin haram da
hada baki wajen aikata babban laifi da karkatar da dukiyar al\’umma da kuma cin amana.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen da aka yi masa.
Hakazalika kotun ta ba da belin wasu mutum ukun da ake tuhumarsu tare da suka hada da
tsohon Ministan makamashi Nuhu Wya da tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kaduna Hamza Ishaq da kuma tsohon shugaban jam\’iyyar PDP na
jihar, Haruna Gayya.
An yi ta yada hoton tsohon gwamnan dauke da allon da aka rubuta sunansa da tuhume-tuhumen da ake masa a kafafen sada zumunta a makon
jiya.
Mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajeren ya ce a ranar Juma\’ar da ta gabata ne EFCC ta gayyaci Ramalan Yero da sauran mutanen don su yi bayani kan zargin karkatar da kimanin naira miliyan 750 wajen yakin neman zabe.