KOTU TA KULLE WANI BABBAN MALAMIN ADDINI A JIHAR OGUN

0
712
Daga Usman Nasidi
WATA kotun majistare da ke zaman ta a garin Ifo dake a jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da umurnin ci gaba da tsare wani babban malamin addinin kirista kuma shugaban majami\’un Holy Garden Ministry mai suna Tobiloba Ipense.
Kamar dai yadda muka samu, kotun dai tana sauraron karar da aka shigar mata inda ake zargin babban malamin da kashe wata masoyiyar sa mai suna Raliat Sanni tare da binne ta a wani boyayyen wuri.
Majiyarmu ta samu labarin cewa tun farko jami\’an \’yan sanda a unguwar Ewekoro ne suka kama babban malamin a ranar 26 ga watan Maris din da ya gabata.
A wani labarin kuma, fitacciyar kungiyar nan ta hadakar \’yan kabilar Yarbawa a Najeriya da aka fi sani da Oodua People’s Congress (OPC) a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana jin dadin ta tare da cikakken goyon bayan ta ga majalisar tarayyar Najeriya game da kudurin ta na tsige shugaba Muhammadu Buhari.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar mai suna Frederick Fasehun wanda kuma majiyar mu ta samu inda a ciki ya bayyana cewa hakan ya zama dole idan dai har ana son demokradiyyar mu ta dore.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here