Daga Usman Nasidi
\’YAN sanda a jihar Naija sun shaida cewa a yau Litinin sun fara daukar matakan zabaro Mutane 200 da suka arce jiya daga wani gindan Yari mai matsakaicin tsaro a Minna ta jihar Naija.
Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Dibal Yakadi, a wata hira da manema labarai ya tabbatar da cewa Firsunoni 19 ne kacal dag cikin 219 suka kai ga kamawa kafin su tsere “Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin mun tabbatar da kamo wadanda suka tsere”.

Sannan kuma ya ce sun aike da wasu jami’ai zuwa tashohin Motoci dake jihar domin kama duk wadanda ke shirin barin garin, a don haka ne yayi kira ga jama’a da su taimaka musu da duk wasu bayanai da zasu taimaka wajen kamo duk wadanda suka tsere din.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu Tsagerun Mahara ne suka kaiwa gidan Kurkukun hari a jiya Lahadi suka kashe wani Ma’aikaci guda da yake bakin aiki a lokacin da kuma wani da yazo wucewa a babur, wanda hakan ya baiwa Fursinonin damar tserewa.