An Rufe Majalisar Tarayya Har Sai 3 Ga Wata Mai Kamawa Na Yuli

0
797
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Daga Usman Nasidi

LABARIN da muke samu daga majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa shugabannin majalisaun tarayyar Najeriya sun sanar da rufe majalisun da suka hada da majalisar dattijai da ta wakilai har sai zuwa ranar 3 ga watan Yuli mai kamawa.

Wannan matakin dai na rufe majalisar kamar yadda mai magana da yawun majalisar ta bayyana an dauke shi ne domin a ba dukkan \’yan majalisar damar gudanar da shagulgulan salla mai zuwa.

Majiyarmu ta samu labarin cewa da suka sanar da matakin rufe majalisar, jami\’an hulda da jama\’a na majalisar sun gode wa \’yan Najeriya tare da rokon su da su ci gaba da yi wa kasa addu\’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here