AUDUGA TA FI KOWANNE AMFANIN GONA SAMAR DA AYYUKAN YI A DUNIYA-FARFESA DADARI

  0
  1450
  Farfesa Salihu Adamu Dadari

  Isah Ahmed, Jos

  A ‘yan kwanakin nan ne Farfesa Salihu Adamu Dadari, malami a sashin bincike da nazarin aikin gona na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya halarci wajen wani taron duniya, kan bunkasa noman auduga da kungiyar kasashen musulmi ta duniya OIC, ta shirya a kasar Turkiya.

  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana abubuwan da suka gudanar a wajen taro, da kuma mahimmancin noman auduga a duniya.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; Mun sami labarin cewa a  ‘yan kwanakin nan ka halarci wani taron duniya, kan noman auduga a kasar Turkiya, mene ne makasudin shirya wannan taro?

  Farfesa Dadari; Wannan taro ne wanda aka shiryawa kasashen da suke cikin kungiyar kasashen musulmi ta OIC,  an shirya shi  ne don  bunkasa  noman auduga  musamman a kasashen da musulmi suka fi yawa.

  Domin a kasashen da musulmi suke ana noman auduga kashi 50 zuwa kashi 60 bisa 100 na audugar da ake nomawa a duniya. Kasashen musulmi kamar siriya da Turkiya da Fakistan duk suna noman auduga sosai.

  Don haka a wajen  wannan taro, wanda aka yi kwanaki uku ana gudanar da shi, an tattauna kan yadda za a tallafa wa manoman auduga a wadannan kasashe da kuma duniya gabaki daya.

  Kuma noman auduga ya zama wajibi a duniya domin shi ne yake bayar da kaya mafi daraja a duniya. Don haka wannan taro ya tattauna yadda za a bunkasa noman auduga a duniya.

  Kuma kasashen da suka halarci wannan taro sun hada da Nijeriya da Sudan da Barkina Faso da Jamhuriyar Benin da Senegal da Nijar da Fakistan da Barkina Faso da jamhuriyar Benin da Azabaijan da  Tajikistan da  da dai sauransu.

  GTK; Wanne irin amfani ne kake ganin Nijeiya za ta yi dangane da wannan taro musamman ta fannin bunkasa noma auduga?

  Farfesa Dadari; Babu shakka Nijeriya za ta amfana da wannan taro, domin tuni mun raba makalolin da aka gabatar a wajen taron zuwa cibiyoyin binciken aikin noma, don kara bincike ta yadda manoman auduga na Nijeriya za su amfana.

  GTK; A matsayinka na masani kan harkokin noma wadanne dalilai ne kake ganin ya sanya gwamnatoci da kungiyoyin duniya suke kokarin ganin an bunkasa harkokin noman auduga a duniya?

  Farfesa Dadari; Wato abin da yake faruwa ka ga kasashen Amerika da Chaina kadai, suna bada kashi  44 bisa 100 na audugar da ake nomawa a duniya. Kuma kamar kasar Indiya tana noma auduga kusan tan miliyan 25 a shekara, saboda masakunta da sauran kasashen waje.  Kuma kamar ita kasar Turkiya noman auduga ne mafi karfin noman da take yi a kasar.

  Ko a nan Afrika kamar kasar Mali da noman auduga suka dogara.

  Kasashen da suka rike noman auduga a duniya suna da yawa saboda mahimmancinta. Ka ga kamar kasar Barazil  da Amerika da Chaina da Indiya da Fakistan suna noma auduga sosai.

  Kuma  a kasashen Afrika kamar Nijeriya da Jamhuriyar Benin da Barkina Faso da Senegal duk suna noman auduga.Domin auduga tana da tasiri a duniya don haka kasashe da dama suke noman auduga a duniya. Shi ya sa kake ganin ake kokarin bunkasa noman audugar.

  Domin auduga  tana bayar da ayyukan yi fiye da kowanne kayayyakin amfanin gona, a duniya. Domin manyan masaku  sun dogara ne da auduga a duniya.  Domin masaka daya za ta iya daukar mutum dubu 50 aiki. Baya ga masu sayar da kayayyakin da masakun suke sakawa da dillalai da masu dako da teloli duk wadannan guraben ayyuka suna tasowa ne daga noman auduga.

  Don haka auduga tafi kowanne amfani gona daraja wajen samar wa masana’antu kayayyakin aiki.

  Ko a nan Nijeriya lokacin da masakun kasar na suke aiki, akwai masaku 13 a garin Kaduna. A lokacin dare da rana mutane ne suke aiki kuma a lokacin mutanen da suke aiki a wadannan masaku sun kai kusan ,miliyan 2.

  GTK; Ganin yanzu mafiya yawan manoman Nijeriya sun rungumi noma kayayyakin abinci ne wadannan irin hanyoyi ne kake ganin za a bi domin manoman nan su rungumi noman auduga?

  Farfesa Dadari; To ka ga idan manomi ya noma masara  ya noma abinci kuma wahalar noman masara bashi da yawa. Amma noman auduga yana da wahala domin za ka yi feshi kusan sau hudu don haka noman auduga yana da wahala.

  Saboda haka gwamnati ta inganta farashin kudadenta kuma ta bude masaku. Ta bai wa manoman auduga rance da iri mai nagarta kuma ta bude kasuwannin sayar da audugar

  GTK; Karshe wanne sako ne kake da shi zuwa ga manoman Nijeriya dangane?

  Farfesa Dadari; Ina yi wa manoman Nijeriya albashir kan cewa idan suka rungumi noman auduga za a sami nasara. Yanzu kamar Dangote yana noman auduga a Nijeriya, kuma  amma yana shigo da ita daga kasar Kamaru. Saboda yana da masaka  maimakon a rika daukar kudadenmu ana kai wa wata kasa ana sayo audugar  gara a bamu kudaden mu rika noman audugar. Don haka ina kira  manoman Nijeriya su rungumi  noman auduga domin yin haka  zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here