Kotu Ta Aika Wa El-Rufa\’i Kashedi Na Karshen A Kan Kin Bin Umarninta

0
644
Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna

Daga Usman Nasidi

WATA babbar kotu da ke zaman ta a Kaduna ta aike wa da Gwamna El-Rufa’i wata takardar kashedin kin yin biyayya ga umarninta. Kotun ta aike da takardar ne ta hannun ofishin sakataren gwamnati da kuma hukumar tattara haraji da raya jihar Kaduna(KADIRS).

Kotun ta aike da takardar ne a matsayin tuni ga takardar umarnin dakatar da gwamnatin jihar Kaduna daga rushe gidan Sanata Suleiman Hunkuyi.

A ranar 28 ga watan Mayu ne hukumar KADIRS ta aike wa Sanata Hunkuyi takardar tunin neman ya biya miliyan N31m na filin gidansa da ya gina duk da kotu ta dakatar da gwamnatin jihar daga daukar wani mataki a kan batun rushe gidan Sanatan.

A ranar 6 ga watan Maris ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da gwamnatin jihar Kaduna da hukumominta daga taba gidan Sanata Hunkuyi da ke fili mai lamba 18A a kan titin Inuwa Wada da ke Unguwar Rimi a garin Kaduna.

Tun da farko, Sanata Hunkuyi ne ya garzaya kotun domin neman ta dakatar da gwamnatin jihar daga yunkurin tan a rushe masa gidansa bayan ta rushe wani gidan nasa da ya bayar ga jam’iyyar APC.

Sai dai gwamnatin jihar ta yi burus da umarnin kotun tare da sake aike wa Sanata Hunkuyi takardar tunin cewa za ta rushe gidansa muddin bai hanzarta biyan harajin Miliyan N31m ga gwamnati ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here