Mata Da Matasa 2000 Masu Rauni Suka Sami Abinci Da Sutura A Sakkwato

0
684
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal sha kwaranniya

GWAMNATIN Jihar Sakkwato ta raba kayayyakin abinci da yaduddukan sutura da kudinsu ya kai Naira Miliyan 23 ga mata da matasa masu nakasa da masu rauni a fadin jihar ta Sakkwato.

Babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin mata, Hajiya A’isha Muhammad ce ta fadi haka a lokacin da take ganawa tare da tattaunawa da manema labarai a ofishinta.

Hajiya A’isha Muhammad ta ci gaba da cewa, daga cikin wadanda suka amfana da wannan tagomashin gwamnatin jihar Saakkwato sun hada da masu fama da cutar kuturta da masu fama da kanjamau (HIV) da Dundumi da kuma uwa-uba marayu.

Ta kara da cewa, akwai mata da dama da suke a gidajen yari daban-daban su ma za su sami wannan tagomashin gwamnatin jihar Sakkwato, domin kuwa an zakulo su ne a mazabun nan guda uku na ‘yan majalisar dattawan Najeriya da suke a Sakkwaton.

Hajiya A’isha Muhammad ta ce gwamnatin jihar ta yanke bayar da wannan tagomashin ne ga wadannan nau’ukan mutane domin su ma su gudanar da bukukuwan salla karama cikin sauki da kwanciyar hankali.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here